Babban Magana: An Kama Marubuciyar Littafin 'Yadda Za Ki Kashe Mijinki' Da Laifin Kashe Mijinta

Babban Magana: An Kama Marubuciyar Littafin 'Yadda Za Ki Kashe Mijinki' Da Laifin Kashe Mijinta

  • Wata kotu da ke Amurka ta kama Nancy Brophy, mawallafiyar wani littafi, ‘Yadda za ki halaka Mijinki’, dumu-dumu da laifin halaka mijinta
  • Dama ta rubuta littafin ne tun a shekarar 2011 inda ta bayyana hanyoyin da mace za ta yi amfani da su wurin halaka mijinta ba tare da an gano ta ba
  • Ana zarginta da harbin mijinta sau biyu ta bayansa sannan masu gabatar da kara sun bayyana yadda Nancy ta siyo bindiga watanni kadan kafin mutuwarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Amurka - Wannan labarin na iya kama da shirin fim, amma da gaske ne, inda wata kotun Amurka ta kama Nancy Brophy - wata marubuciyar wani littafi, ‘Yadda Za Ki Halaka Mijinki’ - dumu-dumu da laifin halaka mijinta.

A 2011, Nancy ta wallafa littafin wanda ta tattaro hanyoyi da dama wadanda mace za ta iya amfani da su wurin halaka mijinta ba tare da an gano ta ba, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

Babban Magana: An Kama Mawallafiyar Littafin 'Yadda Za Ki Kashe Mijinki' Da Laifin Kashe Mijinta
An Kama Mawallafiyar Littafin 'Yadda Za Ki Kashe Mijinki' Da Laifin Kashe Mijinta. Hoto: Fox News.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A watan Yunin 2018, an tsinci gawar mijin Nancy, Daniel Brophy, a Cibiyar Oregon Culinary, inda ya ke koyar da dalibai.

An ga yadda aka harbi Brophy sau biyu a bayansa.

Bayan bincike, ‘yan sanda sun zargi matarsa, wanda hukuncin laifin shi ne zaman gidan yari har karshen rayuwar mutum.

An gan ta a lokacin da aka yi kisan kusa da cibiyar da mijin ke koyarwa

Nancy ta musanta zargin da aka yi mata.

Kamar yadda New York Times ta ruwaito, masu bincike sun gano wani bidiyonta a kusa da cibiyar da ya ke aiki yayin da ta ke tuka motarta kusa da wurin a daidai lokacin da aka yi kisan.

Yayin da aka tambayeta abinda ta ke yi a lokacin, mawallafiyar ta ce ba za ta iya tunawa ba, ta yiwu ta je shan shayi ko kuma yin wasu ‘yan rubuce-rubuce.

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun bayyana shaidar yadda Nancy ta siya bindiga ana saura watanni kadan da mutuwar mijinta kamar yadda The Cable ta nuna.

Nancy ta yi yunkurin boye duk wasu shaidu

Masu gabatar da karar sun sanar da kotu cewa mawallafiyar ta tabbatar da cewa harsasan da ta yi amfani da su ba irin na bindigarta ba ne.

Sun ce Nancy ta amshi garabasar manufofin inshorar rayuwa ana saura kwanaki kadan ta halaka mijinta.

Shawn Overstreet, mataimakin alkalin yankin, ya ce Nancy ce kadai mai burin halaka mijinta.

Sai dai lauyoyin da ke kare ta sun sanar da kotu cewa Nancy da mijinta su na ta shirin yin wata tafiya, inda su ka ce zarginta ake yi da laifin ba tabbaci aka samu ba.

Shaidun da aka gabatar wa kotu a ranar Laraba sun bayyana Nancy a matsayin wacce alamu su ka nuna cewa karara ta yi kisan.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

Za a yanke mata hukunci a ranar 13 ga watan Yuni.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani rahoton, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu , inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel