Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

  • Wani mummunan labarin da muke samu ya bayyana cewa, an samu sabon hari a Rann, inda 'yan ta'adda suka hallaka manoma
  • Wannan na zuwa ne duk da cewa akan samu 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP da ke mika wuya ga sojoji a kasar
  • Rahoto daga majiyoyi sun shaida cewa, akalla manoma 45 aka binne sakamakon harin da ya faru kwanan nan

Rann, Jihar Borno - Mazauna garin Rann, kauyen iyaka a jihar Borno, sun ce da tsakar ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, sun yi jana'izar akalla 45 daga cikin 'yan uwansu da aka kashe a wani hari da wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai wa yankinsu.

Mazauna yankin da suka shaida lamarin sun shaidawa HumAngle cewa suna ci gaba da lalume a ciyayi da ke kusa da su don gano gawarwakin da har yanzu ba a samu ba.

Kara karanta wannan

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

Yadda 'yan Boko Haram suka hallaka manoma a jihar Borno
Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun kashe manoma 45 a wani sabon hari | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge ce, kuma ita ce garin da aka fi tunawa da shi da munanan abubuwan da suka faru na mace-mace a sanadiyyar 'yan ta'adda.

Yadda mummunan lamarin ya faru

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an kai wa manoma da dama da wasu masu gadin gonaki farmaki a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu, yayin da suke gonarsu. 'Yan ta'addar Boko Haram dauke da makamai ne suka kai musu harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta bayyana cewa:

"An kashe manoman ne a lokacin da suke girbe amfanin gonakinsu daga wata gona da ke wajen kauyukan Rann."

Ya ce maharan ba su yi harbi da bindigoginsu ba, sun yi amfani da adduna cikin izza wajen fille kawunan manoman.

Ya kara da cewa:

"Kawai sun sauka kan manoman ne suka kewaye su kuma suka fara kashe su daya bayan daya."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mata da mijin da basu da cin yau balle na gobe sun haifa 'yan 4 reras, suna neman taimako

"Sun yi musu kisan gilla, ta hanyar yanka wuyansu tare da yin kaca-kaca da gawarwakin manoma 45."

Majiyar ta ce an yi jana’izar dukkan manoma 45 da aka kashe da masu gadin gonaki a ranar Litinin.

HumAngle ta tattaro cewa, kimanin mutane 43,000 'yan gudun hijira kuma a halin yanzu suna fama da yunwa a Rann bayan raba su da gidajensu.

Har yanzu dai gwamnatin jihar Borno da jami'an tsaro ba su ce uffan ba kan sabon harin.

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

A wani labarin, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Asabar din da ta gabata, ya ce bai damu da zama abokin tafiyar wani dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.

An ambaci sunan Zulum a cikin wasu batutuwan siyasa a matsayin wanda ka iya zama abokin jiko na gari ga dan takarar shugaban kasa na APC, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata

Zulum ya yi maganar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, wanda ya je Borno domin ganawa da deliget din APC na jihar gabanin zaben fidda gwani na ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel