Na Ce Wa Matata Albashi Na N111k Ne: Mutumin Daya Gina Gida a Sirri Cikin Shekaru 3 Yana Karbar Albashin N666k

Na Ce Wa Matata Albashi Na N111k Ne: Mutumin Daya Gina Gida a Sirri Cikin Shekaru 3 Yana Karbar Albashin N666k

  • Wani mutum ya janyo maganganu a kafar sada zumunta bayan ya labarta yadda ya boye wa matarsa samunsa
  • Yana amsar N666,000 amma sai ya ce mata N111,000 ne albashin sa, ta haka ya samu nasarar ginin gida cikin shekaru 3
  • ‘Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jindadinsu akan yadda mutumin ya yi, yayin da wasu suka dinga yaba masa akan dabararsa

Ghana - Wani matashi dan kasar Ghana ya janyo surutai a kafafen sada zumunta bayan ya fallasa wani lamari da ya dauki shekaru yana boyewa.

A wata wallafa da aka yi a Twitter, an dakko inda wani mai amfani da suna @Accraaaaaa_, ya bayyana yaudarar da ya yi wa matarsa don cimma manufarsa a rayuwa.

Na Fada Wa Matata Albashi Na N111,000 Ne: Mutumin da Ya Gina Gida Cikin Shekaru 3 Yana Amsar Albashi N666,000.
Ma'aikaci cike da annashuwa a fuskarsa. Hoto: DMEPhotography.
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ina Matukar Buƙatar Aure: Ɗan Najeriya Ya Koka Tare Da Wallafa Bidiyon Ɗakinsa Da Kaya a Hargitse

A cewarsa, albashinsa duk wata GHc12,000 matsayin N666,000, amma sai yace wa iyalinsa GHc2,000 wato N111,000 yake amsa inda suka dinga manejin rayuwa.

Ya yi amfani da sauran kudin a kan shi kuma ya gina gidan kansa.

Mutane sun yi caa akan shi

Pinto_Clarks ta jefa masa wata tambaya, inda ta ce:

“Ya za ayi ace kana son mutum kuma ka dinga yi masa boye-boye akan dukiyar ka? Babu so kenan.”

pomzy_mid ta ce:

“Wannan wanne irin haraji kake biya... saboda kirgar kaso 10% kenan na 2k matarka zata dinga. Idan ta gano gaskiya ka shiga uku. Kawai ka fada mata an yi maka karin girma ne.”

its_babymfr ta ce:

“Kai kuwa nawa kake kashewa a ko wacce rana? Matsalar mata kenan. Dama muna neman na kan mu da mun huta.”

Ga wallafar da ya yi a a kasa:

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Kara karanta wannan

Jarumai 5 da ke jan zarensu a masana'antun Kannywood da Nollywood cike da kwarewa

A wani rahoton na Legit.ng, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranarsa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motarsa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel