Elon Musk da Jeff Bezos sun tafka asarar N7.4trn sakamakon rikicin Rasha da Ukraine
- Mashahuran masu kudin duniya guda 2, Elon Musk da Jeff Bezos sun tafka asarar N7.4 tiriliyan daga jimillar dukiyarsu, sakamakon halin da ake ciki a Ukraine
- Elon Musk yayi asarar $13.3 biliyan daga kadarorin sa, inda mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya tafka asarar kimanin $4.41 biliyan
- Kasuwar hannun jarin duniya ta girgiza sakamakon gagarumin tashin hankalin da kasar Ukraine ke ciki, yayin da 'yan kasuwa suka zama masu taka tsan-tsan
Mashahuran masu kudin duniyar nan guda biyu, Elon Musk da Jeff Bezos, sun tafka asarar kimanin N7.4 tiriliyan a rana, yayin da yaki tsakanin Russia da Ukraine yake cigaba da hauhawa.
Mashahuran masu arziki sun tafka asara
A lokacin da mai kamfanin Tesla, Elon Musk yayi asarar daga jimillar dukiyarsa ta sauka zuwa $199 biliyan, bayan yayi asarar $13.3 biliyan, sannan asarar da ya tafka na shekarar ya kai $71.7 biliyan, kamar yadda kididdigar Bloomberg ta bayyana.

Kara karanta wannan
Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

Asali: Getty Images
Ta bangaren hamshakin mai kudi na biyu a fadin duniya, kuma mamallakin kamfanin Amazon, Jeff Bezos, dalilin gagarumin rikici tsakanin Russia da Ukraine ya tafka asarar $5.41 biliyan daga kafatanin tattalin arzirkinsa, hakan yayi kasa da dukiyarsa zuwa $169 biliyan da kuma asarar da ya tafka na $22.0 biliyan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Girgizar tattalin arzirkin nasu yazo ne a lokacin da aka sanar da dakarun kasar Rasha sun fara harba bama-bamai a wasu sassan kasar Ukraine, hakan ya saka firgici a kasuwanni.
Kasuwar crypto da girgiza matuka a safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, 2022. Darajar man fetur kuwa, ya hauhawa zuwa kimanin $100 duk ganga daya saboda tsananin tashin hankali tsakanin Rasha da Ukraine.
Cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote ya samu N217.5bn, ya tsallake biloniyoyi 6 na duniya a jerin masu arziki
A wani labari na daban, Aliko Dangote, hamshakin mai arziki kuma wanda ya fi kowa kudi a Afrika ya samu karin N217.5 biliyan a dunkiyarsa cikin sa'o'i 8 kacal inda ya zama mutum na 91 mafi arziki a duniya.

Kara karanta wannan
A Cikin Awa 24 Kacal, Ɗangote Ya Samu Kuɗin Da Ya Ɗara Na Elon Musk Da Bill Gates
Kamar yadda Bloomberg ta bayyana, Dangote a halin yanzu arzikinsa ya kai $20.1 wanda ya kai kashi 5.23 na ma'adanar Najeriya ta kasashen ketare mai jimillar kudi har $40.1 biliyan.
Hauhawar farashin hannun jari a kamfanin simintin Dangote, karuwar kudin mai da kuma farashin taki ya taimaki dan kasuwan Najeriyan mai shekaru 64 a duniya.
Asali: Legit.ng