Innalillahi: Mata 13 Sun Mutu Bayan Rufta Wa Cikin Rijiya a Wurin Bikin Ɗaurin Aure

Innalillahi: Mata 13 Sun Mutu Bayan Rufta Wa Cikin Rijiya a Wurin Bikin Ɗaurin Aure

  • Wasu mayan mata da yara mata 13 sun riga mu gidan gaskiya bayan sun fada wani rijiya yayin bikin aure a India
  • Wadanda abin ya faru da su suna zaune ne a kan murfin karfe da ya rufe rijiyar a ranar Laraba kwatsam sai ya rufta da su
  • Farai Ministan India, Narendra Modi, ya kwantanta lamarin da abin tada hankali ya kuma ce jami'an gwamnati na can suna bada taimako

India - Manyan mata da yara mata 13 sun mutu bayan tsautsayi ya yi sanadi sun fada rijiya yayin bikin aure a arewacin India, yan sanda suka sanar a ranar Alhamis, rahoton Channels TV.

Wadanda abin ya faru da su suna zaune ne a kan wani murfin karfe da ya rufe rijiyar a ranar Laraba kwatsam sai ya rufta, babban jami'in dan sanda Akhil Kumar ya shaidawa manema labarai a Kushinagar, Jihar Uttar Pradesh.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata

Innalillahi: Mata 13 Sun Mutu Bayan Rufta Wa Cikin Rijiya a Wurin Bikin Ɗaurin Aure
Mata 13 sun rufta rijiya sun mutu yayin bikin aure. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channels TV ta rahoto cewa Babban alkakin yankin, S. Rajalingam ya ce tsohuwar rijiya ce don haka ta kasa dauka nauyin wadanda suka zauna a murfin ta.

"Wadanda abin ya faru da su sun fada cikin rijiyan kuma burbushin murfin ya danne su," in ji shi.

Manyan matan da yara matan sun taru ne domin hallartar wani bikin aure a kauyensu.

Farai Minista Modi ya yi alhinin rasuwar matan

Farai Minista Narendra Modi ya ce wannan lamari ne mai 'sosa zuciya'.

"Mahukunta a yankin suna can suna bada duk taimakon da ya kamata," kamar yadda ya rubuta a Twitter.

Bisa al'ada, daurin aure babban lamari ne a India inda mutane da dama ke taruwa ana shan biki na tsawon kwanaki.

A shekarar 2017, wasu mutane da za su tafi daurin aure su 24 sun mutu bayan katanga ya rufta musu yayin da ake ruwan sama a Jihar Rajasthan.

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel