UAE ta sanar da ranar ɗage takunkumin shiga ƙasar ga ƴan Najeriya

UAE ta sanar da ranar ɗage takunkumin shiga ƙasar ga ƴan Najeriya

  • Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar UAE ta ce za ta fara barin 'yan Najeriya da wasu kasashen Afrika 11 shiga kasar daga ranar Asabar mai zuwa
  • Sai dai, ta sanar da cewa ta gyara tsarin shiga kasar na fasinjoji daga kasar Uganda, Rwanda da kasar Ghana
  • Ta kara da kira ga duk fasinjoji da matukar suka ji wata alama ta cutar korona, toh su tabbatar sun gujewa yunkurin shiga kasar

Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ta ce za ta cigaba da barin fasinjoji daga kasashen Afrika 12 da suka hada da Najeriya shiga kasar daga ranar Asabar, 29 ga watan Janairu.

Hukumar taimakon gaggawa ta kasar UAE, NCEMA, ta sanar da hakan ne a wata wallafa da ta yi a shafin ta na Twitter a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta soke sababbin gyare-gyaren da Majalisa tayi a kasafin kudin 2022

UAE ta sanar da ranar ɗage takunkumin shiga ƙasar ga ƴan Najeriya
UAE ta sanar da ranar ɗage takunkumin shiga ƙasar ga ƴan Najeriya. Hoto daga Valery Sharifulin TASS
Asali: Getty Images

"Daga ranar 29 ga watan Janairu, UAE za ta karba fasinjoji daga kasashen Kenya, Tanzania, Ethiopia, jamhuriyar Congo, Afrika ta kudu, Botswana, Eswatini, Lesotho, Mozambique, Namibia da Zimbabwe," wallafar ta ce.

Kamar yadda takardar tace, an sake gyara tsarin shiga kasar ga jiragen da za su taso daga kasashen Ghana, Rwanda da Uganda.

Ta kara da cewa, fasinjojin da ke isa daga kasashen nan uku zuwa UAE dole ne su kasance sun yi gwajin korona a cikin sa'a'o'i 48 daga barin kasar su zuwa UAE.

Hukumomi a UAE sun ce dole ne fasinjoji su kasance an yi musu gwajin PCR a filayen sauka da tashin jiragen sama na kasar su kuma UAE za ta sake yi musu wani bayan isar su.

Kara karanta wannan

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Kasar Larbawan ta bukaci mazauna kasahen Afrika da su guje shiga kasar su matukar sun san suna dauke da wasu alamomin cutar korona.

UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19

A wani labari na daban, gwamnatin daular Larabawa (UAE) ta dakatar da shigar da 'yan Najeriya zuwa Dubai a matsayin hanyar dakatar da yaduwar cutar COVID-19.

Wannan umarnin ya biyo bayan sa'o'i 24 da da jiragen UAE suka sanar da wannan dakatarwar jirage daga Legas zuwa Abuja.

Babban jirgin da yake kai mutane Dubai daga Najeriya, Air Peace, ya sanar da wannan umarnin na UAE ga fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel