Gwamnatin Buhari ta soke sababbin gyare-gyaren da Majalisa tayi a kasafin kudin 2022

Gwamnatin Buhari ta soke sababbin gyare-gyaren da Majalisa tayi a kasafin kudin 2022

  • Majalisar zartarwa ta tarayya ta karbi wasu gyare-gyare da ‘Yan majalisa suka yi wa kasafin 2022
  • Akwai wasu shawarwari da kwaskwariman da aka yi wa kasafin da majalisar FEC tayi watsi da su
  • Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta bada dalilin da ya sa ta gagara daukar shawarwarin na su

FCT Abuja – Rahotanni sun zo cewa Majalisar zartarwa ta kasa watau FEC ta amince da wasu gyare-gyaren da aka yi wa kundin kasafin kudin shekarar 2022.

‘Yan majalisar tarayya sun yi wasu kwaskwarima a kundin kasafin kudin da Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar masu a 2021.

Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi, Zainab Ahmed ta ce gyaran da ‘yan majalisar suka yi zai iya yin tasiri kan dokokin da suka kafa EFCC da NFIU.

Kara karanta wannan

Baturiya mai auren ‘Dan Najeriya ta rangada ado, ta ci ankon atamfa da yara da mai gidanta

Daily Trust ta rahoto Zainab Ahmed ta na cewa za a dawo da wasu kudi da ‘yan majalisa suka cire a kasafin kudin kasar, adadin wadannan kudi ya haura N100bn.

Gwamnatin tarayya ta ce an saba doka idan aka amince da wadannan canji da majalisa ta kawo.

Sashen dokar da aka yi wa kwaskwarima za ta ba hukumomin EFCC da na NFIU damar karbar 10% na duk abin da suka karbo daga hannun barayin kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasafin kudin 2022
Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi, Zainab Ahmed Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ba za ta yiwu ba

“Mu na neman a soke wannan sauyi saboda zai zama ya ci karo da dokokin da suka kafa aikin wadannan hukumomi biyu, kuma ya saba dokar tattali ta 2021.”
“A gefe guda, dayan kari na 11 da aka yi yana cewa a kyale ofisoshin jakadancin Najeriya su rika cire kudin ayyuka ba tare da izinin ma’aikatar kasar waje ba.”

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Blueprint ta rahoto Ministar ta na cewa amincewa da wannan bangare ya saba dokokin Najeriya.

Da take bayani, Ministar kudin ta fadawa ‘yan jarida cewa majalisar FEC ta amince da wata doka da za ta karfafa alakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Afrika ta kudu.

Wannan doka za ta taimaka wajen bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen biyu, kuma za su rika taimakawa junansu da bayanan da za su kara samar da hadin-kan juna.

AfDB a kamfanin Dangote

Kwan nan aka ji shugaban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina ya kai ziyara zuwa matatar Aliko Dangote, wanda zai yi sanaddiyar samun ayyuka 38000.

Akinwumi Adesina ya yaba da wannan gagarumin aiki da babban mai kudin na Afrika ya dauko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel