Latuka: Kabilar da saurayi ke sace budurwa kafin ya aure ta, daga baya ya sanar da mahaifinta

Latuka: Kabilar da saurayi ke sace budurwa kafin ya aure ta, daga baya ya sanar da mahaifinta

  • Yayin da a wasu bangarori na duniya saurayi ya ke bibiyar budurwar da yake so har ta amince da aurensa sannan ya nemi izinin iyayenta, abin ya sha bambam da kabilar Latuka da ke kudancin Sudan
  • A al’adarsu, dole ne saurayi ya sace budurwar da yake so ya aura tare da gayyatar wasu mazan da zasu taya shi mamayar budurwar sannan su kamo ta su tsere da ita
  • Bayan sace ta su na zarcewa da ita gidan saurayin da ke niyyar aurenta, sannan daga bisani su nemi izinin mahaifinta, daga nan mahaifin budurwar zai lakada wa saurayin duka, matsayin amincewarsa

Sudan - A wasu bangarori na kasashen duniya, dole sai saurayi ya bi budurwar da yake so ya aura don ta amince daga bisani sai ya nemi izinin iyayenta, amma abin ya sha bambam da kabilar Latuka da ke kudancin Sudan, Pulse NG ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Bisa al’adarsu, wajibi ne mai neman aure ya sace budurwar da yake son ya aura tare da neman taimakon wasu kattin wadanda zasu taru su kamo budurwar.

Latuka: Kabilar da saurayi ke sace budurwa kafin ya aure ta, daga baya ya sanar da mahaifinta
Kabilar Latuka: Kafin saurayi ya auri budurwa, sai ya sace ta sannan ya sanar da mahaifinta daga baya. Hoto: Pulse NG
Asali: Facebook

Bayan kama ta, zasu wuce da ita gidan saurayin inda za a ajiyeta sannan daga bisani a sanar da mahaifinta cewa tana hannunsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan mahaifinta ya amince zai zane saurayin da ke son auren diyarsa

Kamar yadda Pulse NG ta bayyana, ba wannan kadai bane abinda zai bayar da mamaki ba, sai mahaifin budurwar ya zane saurayin da ke shirin auren diyarsa, hakan ne alamun amincewarsa.

Ba dai a tabbatar da yawan dukan da mahaifinta zai masa ba, amma da zarar an sace budurwa shi kenan za ta hakura ta amince da zama da saurayin da ya sace ta har karshen rayuwarta.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

A wasu bangarorin na duniya, a natse ake bi a hankali inda iyaye su ke mika auren diyarsu ga saurayi, kuma ya na tabbata ne bayan mata da mijin sun amince da juna, amma ga Latuka kuwa akasin hakan ne.

Bayan satar budurwar, mai neman auren yarinyar ba zai mayar da ita ga iyayenta ba, zai fara zuwa wurin mahaifinta tare da wani babba a danginsa daga nan su nemi aurenta.

Ko mahaifin ya amince ko bai amince ba auren zai tabbata

Daga baya mahaifin zai bayyana amincewarsa ko akasin hakan. Zai zane saurayin wanda shi ne zai auri diyarsa, idan har ya amince da auren.

Sannan idan mahaifinta ya ki amincewa, saurayin ne zai yanke shawarar abinda zai yi, ko ya mayar da budurwar ko kuma ya aureta.

Mutane na ci gaba da cece-kuce akan rashin ba budurwa zabi akan auren wanda take so ko kuma ta ci gaba da rayuwarta tare da shi.

Kara karanta wannan

Hukuncin fadan ‘Happy Xmas’ ga kiristoci a musulunci daga bakin Dr. Sani Rijiyar-Lemu

Kabilar sun shahara wurin noma da kiwo

Kabilar Latuka ko Otuho sun shahara da noma da kiwo tun ba yanzu ba. Su na kiwon shanu, tumaki da akuyoyi a tsaunukan kudancin Sudan sannan su na noman gyada, gero, masara, doya da rogo.

‘Yan kabilar Latuka ba sa da shugabanni, kowa kawai rayuwarsa yake yi, sai manyan su masu shekaru ne su ke shimfida musu dokoki.

Kabila ce wacce ba ta yarda da wani addini ko kuma kabila ta daban ba. Tsawon shekaru duk da yadda mutane suke sukar salon neman aurensu sun ki sauya tsarin.

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel