Hukuncin fadan ‘Happy Xmas’ ga kiristoci a musulunci daga bakin Dr. Sani Rijiyar-Lemu

Hukuncin fadan ‘Happy Xmas’ ga kiristoci a musulunci daga bakin Dr. Sani Rijiyar-Lemu

  • Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya maida martani ga masu inkarin haramta taya kiristoci murnar bikin kirismeti
  • A wani karatu da ya yi kwanaki, Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yace babu mazhabar da ta yarda da murnar bikin nasara
  • Shehin yace ana so a samu kyakkyawar zamantakewa da kiristoci, ba tare da an taya su murnar yin bikin addinin na su ba

Gidan talabijin na Africa TV 3 sun dauko karatun Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu, inda ya kawo maganganun shehunnai a game da wannan mas’alar.

“Abin da aka sani a kaf kafuwar tarihin Musulunci da duk mazhabar Musulunci (limamai hudu), abin da yake rubuce a cikinsu shi ne haramcin wannan.”
“A duk wata mazhaba da aka samu a Duniya da aka san ta tuni da sauran mazhabobi, abin da ke a littafansu shi ne haramun ne taya wani mai idin kafirci murna.”

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

Babban malamin na Kano ya kawo maganar Ibn Qayyim Al-Jawzy wanda ya kamanta taya mai bautar gumaka murna da mutum ya yi wa gunki ibada da kansa.

Shehin yace za a iya tuna wanda ba musulmi ba murna idan ya samu karuwar Duniya, ko ayi masa jaje idan hadari ya faru da shi, akasin abin da ya shafi addini.

A cewar Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu, abin da musulunci ya bada umarni shi ne Bayin Allah su bar kowa ya yi addininsa, ba tare da an tursasawa kowa ba.

Dr. Sani Rijiyar-Lemu
Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu Hoto: @Drmuhdsaniumarmusa
Asali: Facebook

Abin babban lamari ne - Sani Umar Rijiyar Lemu

Abin da Allah (SWT) Ya fada shi ne yin shirka kamar zagin Ubangiji ne wanda babban lamari ne a addini, don haka bai kamata a taya kirista yin bikin kirismeti ba.

Kara karanta wannan

Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

Malamin yake cewa akwai malamai irinsu Mansur Kayali masu rubabben tunanin da suke cewa duk wanda bai taya masu yin kirismeti murna ba zai shiga wuta.

A raddin da yake yi wa Kayali, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemu yace duk wanda bai yi imani da Manzon Allah (SAW) ba, makomarsa za ta kasance jahannama.

Sani Rijiyar Lemu ya kara da cewa mabiya sauran addinai ba su saba taya musulmai murnar bukukuwansu ba, akasin abin da wasu musulmai suke yi masu yau.

A karshe shehin yace a darikun junansu, kiristocin da ba su yarda da bikin kirismeti ba, ba su taya su murna, yace ana neman a daina jin sunan Allah a ban-kasa.

'Yan bindiga sun yi ta'adi a Zaria

Kwanaki aka ji an dauke akalla mutane shida a yankin Wusasa, garin Zaria, jihar Kaduna a daren bikin kirismeti, har yanzu babu labarin inda 'yan bindiga su ka kai su.

Kara karanta wannan

Kungiyar MSSN ta fusata da yadda ake kuntatawa masu hijabi a kudu, za ta dauki mataki

Da kimanin karfe 10:30 miyagun ‘yan bindiga suka shigo garin Wusasa, suka rika bi gida zuwa gida domin su dauke Bayin Allah, har da iyalin wani jami'in 'dan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel