Mutumin da aka kora daga makaranta ya mallaki N32trn, ya zama mafi arziki a China

Mutumin da aka kora daga makaranta ya mallaki N32trn, ya zama mafi arziki a China

  • Zhong Shanshan wanda ya fara sayar da ruwan gora a shekarar 1960 da doriya ya zama mutum mafi kudi a kasar China bayan ya ture Jack Ma, mamallakin Alibaba
  • Kasuwancinsa ya bunkasa ne lokacin annobar COVID-19 inda ya fara sayar da abubuwan awon cutar, hakan ya daga yawan dukiyarsa
  • Ya bar makaranta yana da shekaru 12 inda ya koma leburanci da aikin kafinta sai kuma ya fara sana’ar jarida kafin ya koma sayar da ruwan gora

China - Idan daukaka ta zo wa mutum, kowanne irin aiki ko sana’a ya je yi sai ya bunkasa fiye da tunanin jama’a.

Sana’ar ruwan gora Zhong Shanshan ya fara, yanzu haka ya zama mutum mafi dukiya a kasar China inda ya ke da Naira tiriliyan 32.1 daidai da dala biliyan 77.4 inda mai Alibaba, Jack Ma ya koma kasan sa inda ya ke da Naira tiriliyan 16.06 daidai da dala biliyan 38.7.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

Mutumin da aka kora daga makaranta ya mallaki N32trn, ya zama mafi arziki a China
Mutumin da aka kora daga makaranta ya mallaki N32trn, ya zama mafi arziki a China. Hoto daga bloomberg.com
Asali: UGC

Kididdigar Bloomberg’s Billionaires ta gano cewa dukiyar Shanshan ta zarce naira tiriliyan 40.

Shanshan ne mai ruwan gorar Nongfy Spring da kuma Wantai Biological Pharmacy Enterprise a Shanghai.

Dukiyarsa ta karu yayin korona

Lokacin annobar COVID-19 dukiyarsa ta habaka inda ya koma sayar da kayan gwajin cutar.

Asalin silar dukiyarsa ita ce harkar ruwan gora wacce ya dade yana yi har ya zama biloniya yayin da kamfaninsa ya shiga cikin jerin Hong Kong Stock Exchange a ranar 20 ga watan Satumban 2020.

Inda ya sa kudadensa sun hada da Yangshengtang da Hangzhou Youfu kamar yadda rahoton kamfanin na kowacce shekara ya nuna.

Dukiyarsa ta karu da naira tiriliyan 13.2.

Shanshan ma yana hada kayan gwajin hepatitis a China, Beijing na Wantai Pharmacy Enterprise, wanda kowa ya san Zhong ya na hadawa.

Kara karanta wannan

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

A shekarar 2021 rahoton kamfanin na kusan duk shekara ya bayyana yadda ya mallake shi ta Yengshentang.

Indian Times ta ruwaito cewa, a 1980 da doriya Zhong ya zama dan jarida. Daga baya ya fara sana’ar ruwan gora a kudancin China, Haina, bayan kwashe shekaru 5 ya na harkar jarida.

Ya bar makaranta kamar yadda Zuckerberg da Buffet Zhong suka bar makaranta yana da shekaru 12 ya fara aikin lebura daga baya kuma ya zama kafinta.

Shanshan ya fadi jarabawar shiga jami’a ta JAMB har sau biyu kafin ya shiga Open University of China.

Shugaban Koriya ta arewa ya haramta dariya na tsawon kwana 11 a ƙasar

A wani labari na daban, Shugaban kasar Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya haramta wa 'yan kasar sa nuna kowacce irin al'amari farin ciki na tsawon kwanaki 11 domin cikar shekaru 10 da rasuwar Kim Jong-Il.

Kamar yadda rahotannin The Telegraph suka bayyana, wannan alamun nuna farin cikin sun haramta a bayyana su kama daga dariya ko shan giya na tsawon kwanaki 11 domin makoki.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Asali: Legit.ng

Online view pixel