Omicron: An samu wasu da suka zo Najeriya dauke da sabon samfurin Coronavirus

Omicron: An samu wasu da suka zo Najeriya dauke da sabon samfurin Coronavirus

  • Sabon nau’in Coronavirus ya shiga kasar Kanada, akalla mutane biyu sun kamu da cutar a yanzu
  • Ministan kiwon lafiya na Kanada, Jean-Yves Duclos ya tabbatar da wannan a wani jawabi da ya fitar
  • Wadanda aka samu dauke da cutar wasu mutane biyu ne wanda sun ziyaci Najeriya kwanan nan

Canada - A ranar Lahadi, 28 ga watan Nuwamba, 2021, kasar Kanada ta ce ta samu bullar sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 wanda aka fi sani da Omicron.

Gidan talabijin na NBC News ya fitar da rahoto cewa wadannan mutane biyu da aka samu da cutar sun ziyarci Najeriya a ‘yan kwanakin nan da cutar ta rikide.

Gwamnatin Ontario ta tabbatar da wannan lamarin, ta ce wadanda aka gano su na dauke da samfurin na Omicron, su na zaune a babban birnin jihar na Ottawa.

Tuni jami’an tarayya da na jiha suka killace wadannan Bayin Allah, yayin da ma’aikatan lafiya suke kokarin gano wadanda duk su ka samu alaka da su a Kanada.

Ministan lafiya na kasar Kanada, Mista Jean-Yves Duclos, ya fitar da jawabi na musamman.

Omicron - Coronavirus
Ana gwajin COVID-19 Hoto: en.as.com
Asali: UGC

Jawabin Ministan kiwon lafiya, Jean-Yves Duclos

Jean-Yves Duclos ya bayyana cewa hukumomin lafiya za su cigaba da sa ido domin akwai yiwuwar a samu karuwar wannan cuta ta murar mashako a kasar.

“Hukumar lafiyar jama’a ta Kanada ta sanar da ni game da gwaji da killace wasu mutane biyu masu dauke da samfurin COVID-19 na Omicron a Ontario.”
“Yayin da ake cigaba da gwaji da duba su, ana tunanin za a cigaba da samun masu dauke da samfurin wannan cuta a kasar Kanada.” - Jean-Yves Duclos

Najeriya ta tsira kawo yanzu

Jaridar Punch tace har zuwa yanzu an tabbatar da cewa babu mai nau’in Omicron a Najeriya.

Tun a ranar Juma’ar da ta wuce, gwamnatin Kanada ta hana shiga kasashe bakwai a Afrika. Najeriya ba ta cikin wadannan kasa da ake shakka a halin yanzu.

Ingila ta toshe kasashe Kudancin Afrika

A makon da ya wuce aka ji gwamnatin Kasar Ingila ta haramta zuwa wasu kasashen Afrika saboda gudun annobar COVID-19 da ta saki rikida a samufin B.1.1.529.

Dokar za ta shafi kasashen Afrika ta Kudu, Botswana, Lesotho, Eswatini, Zimbabwe da Nambiya. Wannan takunkumi da aka sa ya fara aiki ne daga daren Ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel