‘Yan bindiga sun saki mutane 10 da suka yi garkuwa da su a Zaria bayan an biya N40m

‘Yan bindiga sun saki mutane 10 da suka yi garkuwa da su a Zaria bayan an biya N40m

  • Bayan tsawon kwanaki a tsare, ‘Yan sanda sun ce an fito da wasu ma’aikatan garin Zaria da aka sace
  • ‘Yan bindiga ne suka yi garkuwa da wadannan mutane a wajen gaisuwar mutuwa a kauyen Giwa
  • Sai da ‘yanuwa da abokan arziki suka biya kudin fansar N40m, amma har yanzu wasu su na tsare

Kaduna - Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun tabbatar da cewa mutane 10 a cikin ma’aikatan karamar hukumar Zaria su 13 da aka yi garkuwa da su, sun fito.

Jaridar Premium Times tace kakakin ‘yan sanda na jihar Kaduna, SP Mohammed Jalinge ya shaidawa manema labarai wannan a ranar Lahadi, a garin Zaria.

Mohammed Jalige yace ‘yan sanda su na kokarin kubutar da ragowar mutane ukun da ke tsare.

Rahotanni daga Vanguard da Tribune sun tabbatar da cewa sai da aka biya ‘yan bindigan da suka dauke wadannan ma’aikata Naira miliyan 40 kafin a fito da su.

Kara karanta wannan

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

Wata majiya ta shaidawa ‘yan jarida cewa ‘yan uwan wadanda aka dauke ne suka tara kudin fansar bayan sun shafe kwana da kwanaki a hannun miyagun.

‘Yan bindiga
Gungun wasu 'Yan bindiga Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wasu mutane uku na tsare

Ragowar ukun su na tsare har yanzu domin cikin sharudan da miyagun ‘yan bindigan su ka bada kafi su saki mutanen, sai an kawo masu sababbin babura uku.

“Wadanda aka fito da su ba su hadu da iyalansu ba tukuna domin an kai su wani asibiti domin a duba lafiyar jikinsu.”
“Kudin kurum aka kai masu, shiyasa ba su saki ragowar ma’aikata ukun ba.” – Majiya.

Shugaban karamar hukuma ya yi gum

Hukumar dillacin labarai ta kasa ta tuntubi shugaban karamar hukumar Zariya, Injiniya Aliyu Ibrahim, inda yace babu abin da zai iya kara cewa a kan labarin.

Kara karanta wannan

Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu

Aliyu Ibrahim wanda aka fi sani da ‘Magani sai da gwaji’ ya ki yin karin bayani kan yiwuwar gwamnati ta taimakawa iyalan wadanda aka sace da sayen babura.

Yadda za a zauna lafiya

A farkon makon nan ne aka ji cewa GoodluckJonathan wanda ya yi mulki tsakanin 2010 da 2015 ya ba shugabanni shawarar yadda za a samu zaman lafiya a Najeriya.

Jonathan yana ganin kasar nan za ta zauna lafiya idan shugabanni suka dauki kowa a matsayin daya, yace wannan zai kawo karshen korafe-korafen da wasu ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel