Babban ‘Dan Sarki Aminu Ado Bayero ya nemi auren ‘Yar fitaccen Attajirin Sokoto

Babban ‘Dan Sarki Aminu Ado Bayero ya nemi auren ‘Yar fitaccen Attajirin Sokoto

  • Kabiru Bayero zai auri ‘diyar babban attajiri kuma ‘dan kasuwar garin Sokoto, Ummarun Kwabo.
  • Alhaji Kabiru Bayero ya nemi auren Aisha Ummarun Kwabo a gidan gwamnatin jihar Sokoto dazu
  • Wazirin kasar Kano, Alhaji Sa’ad Gidado ya jagoranci tawagar Sarkin da ta nemawa saurayin aure

Kano - Kabiru Bayero, ‘dan Mai martaba Aminu Ado Bayero ya nemi auren ‘yar fitaccen attajiri kuma ‘dan siyasar Sokoto, Ummarun Kwabo.

Kabiru Bayero wanda shi ne babban yaron Sarkin Kano Aminu Ado Bayero zai auri ‘yar Ummarun Kwabo.

Jaridar Daily Nigerian ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, 2021 cewa tawagar Sarakan Kano da kasar Bichi sun isa garin Sokoto.

Kabiru Bayero wanda ya karanta ilmin kasuwanci a jami’a ne zai aauri Aisha Ummarun Kwabo.

Kara karanta wannan

Jafar Jafar: Bayan wata 5, Ganduje ya biya ‘dan jaridar da ya bankado ‘faifan dala’ N800, 000

Sarki Aminu Ado Bayero
Aminu Ado Bayero Hoto: @sanimaikatangaweddingevents
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tawagar Kano da ta je baiko a Sokoto

Wazirin Kano, Sa’ad Gidado ya jagoranci tawagar da ta hada da Sarkin Dawaki Maituta Kano, Abubakar Bello Tuta; da Dan Isan Kano, Kabiru Tijjani Hashim.

Rahoton yace sauran ‘yan tawagar su ne Dandarman Kano, baffan yaron watau Alhaji Bello Bayero da kuma Kachallan Kano, Alhaji Magaji Galadima.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto, an nemi auren budurwar ne a gidan gwamnan jihar Sokoto.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ne ya amince da baikon, ya yarda ‘dan Sarkin ya nemi auren Aisha Ummarun Kwabo.

Mal alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya samu wakilcin Wazirin Sokoto, Alhaji Sambo Junaidu a wajen neman auren da aka yi.

An biya N250, 000 a matsayin sadaki kafin a daure auren, abin da ya rage shi ne a sa ranar biki.

Kara karanta wannan

Hotuna: Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote

Asali: Legit.ng

Online view pixel