A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi
- Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya bada shawara kan yadda za'a magance matsalar tsaro
- A ra'ayinsa wannan shine mataki daya tilo da zai taimaka matuka
- Duk matashin da ya shiga harkar zai samu lambar yabo ta musamman
Ibadan - Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa lamarin tsaron Najeriya ya yi tsamarin da ya kamata a nemo sabbin hanyoyin maganceta da wuri.
Yayi jawabi a wani taro a Ibadan, Fayemi ya yi kira ga yan siyasa su daina siyasantar da lamarin tsaro saboda kamata yayi a hada kai wajen gyara kasar ba lalata ta ba.
Kamfanin dillancin Najeriya NAN ta ruwaito Fayemi da cewa Najeriya na bukatar zakakuran matasa masu kishin Najeriya domin kawar da matsalar da muke ciki.
A cewarsa, hanya daya tilo da za'a bi shine daukan matasa da dama cikin aikin yan sanda da Soji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yi amfani da matasan NYSC
A shawarar da ya bada, hanya mafi sauki yanzu shine a yiwa dokar shirin bautar kasa NYSC gyaran fuska.
Gwamnan yace za'a iya amfani da sansanin horar NYSC dake fadin tarayya matsayin wajen horar da matasan aikin Soja.
Yace wadanda ba za suyi ba kuma kada a biyasu kudin albashi, suyi bautar kasa kyauta.
Yace:
"Ta wannan hanyar, za'a iya amfani da kudin da ake kashewa NYSC da kuma wani kari."
"Wadanda suka ki yarda shiga faggen yaki kuma suyi bautar kasa kyauta, idan ya zama wajibi a cigaba da shirin NYSC."
"Hanyar janyo hankalin mutane shiga harkar shine basu lambar yabo da satifiket na musamman, sannan kuma a tabbatar musu da aikin Soja ko aikin gwamnati idan suka kammala bautar kasa."
Fayemi ya ce duk da halin da ake ciki yanzu, Najeriya za ta fita daga cikin wannan hali da take ciki.
An kashe mutane fiye da 1, 300 yayin da Fadar Shugaban kasa ta ke cewa ana samun tsaro
A bangare guda, mutane akalla 1, 153 aka hallaka, baya ga sojoji 105, ‘yan sanda 67 da jami’an kula da shiga da fice biyu da jami’in kwastam suka mutu a wata uku.
Wani bincike da kungiyar SBM Intelligence ta gudanar ya nuna cewa mutane kusan 1, 200 suka mutu tsakanin watan Yuli da Satumban 2021 a fadin Najeriya.
Jaridar Daily Trust tace ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram da ‘yan bindiga da sauran masu tada-tsaye ake zargi da laifin hallaka dubban mutane a jihohin kasar.
Asali: Legit.ng