Facebook zai fara daukar mataki kan masu yada abubuwan batanci kan 'yan siyasa

Facebook zai fara daukar mataki kan masu yada abubuwan batanci kan 'yan siyasa

  • Kamfanin Facebook ya shirya tsaf don kau da yada lalata a kafar ta Facebook da kewayenta
  • Kamfanin ya bayyana wasu abubuwan da zai fara daukar mataki a kansu daga mutanen kafar
  • Ya bayyana wannan matakin ne domin kare martabar shahararrun mutane a kafar sada zumunta

Shaharraren kamfanin nan na sada zumunta, wato manhajar Facebook, ya sanar da sabbin ka'idojin da ya fitar na gogewa da hana rubutu ko kalaman batanci ga manyan mutane a kan shafukan Facebook.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwar da Facebook ta fitar ta hannun Antigone Davis, wacce Legit.ng Hausa ta samo, inda aka bayyana dalla-dalla manufar shigo da sabuwar dokar.

Facebook zai fara goge rubutun da ke taba martabar 'yan siyasa da manyan mutane
Matakan da Facebook zai dauka kan masu yada batsa | Hoto: about.fb.com
Source: UGC

Kamfanin Facebook ya yi bayanin cewa, manhajarsa kafa ce ta sada zumunta da ke yada kauna da zaman lafiya, don haka ba zai yarda da batanci kan wasu daidaikun mutane ba, wannan ne dalilin daukar matakin.

Read also

Abubuwan da ya kamata ku sani game da sakonnin da mutane ke yaɗawa a dandalin WhatsApp

A cewarsa, zama dan siyasa ko shahararren mutum ba zabi bane ga mutum, wanda hakan kan jawo yawaitar jin kalamai marasa dadi daga mutane daban-daban.

Jerin laifukan da Facebook zai dauki mataki a kai

Da yake jero irin matakan da zai dauka, Facebook ya ce ba zai lamunci irin wadannan abubuwa ba kamar haka:

  1. Rubutun da ke da alaka da batsa tsagwaransu
  2. Asusun mutane, shafuka, dandali ko taron da ke da alaka da batanci ga wani shahararren mutum ta fuskar batsa
  3. Hotuna masu nuna abin gyama, hotuna da zane-zane na batsa
  4. Hari ta hanyar kwatanta munin jiki wadanda aka ta'allaka da mutum, ambata shi ko sanya su akan asusun shahararrun mutane
  5. Yada abubuwan da ke nuna aikata wani aiki na batsa

Hakazalika, Facebook ya ce ya hada kai da dandazon masu bashi gudunmawa daga cikin al'umma don tabbatar da gogewa da hana faruwar irin wadannan abubuwan.

Read also

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi

A baya kuwa, wanda ya kirkiro kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da dakatar da kafar, inda ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Lamarin da ya janyo asarar ta auku ne cikin sa’o’i kadan kwatsam kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook, Facebook Messenger, Instagram da WhatsApp su ka tsaya cak su ka dena yin aiki.

Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.

Source: Legit

Online view pixel