'Yan sandan Kenya Sun Cafke Shugaban Kamfanin Binance da Ya Tsere a Najeriya

'Yan sandan Kenya Sun Cafke Shugaban Kamfanin Binance da Ya Tsere a Najeriya

  • Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta kama daya daga shugabannin Binance, Nadeem Anjarwalla da ya tsere daga Najeriya inda ya ke fuskantar shari'a
  • Ana tuhumar kamfanin na Binance da gudanar da hada-hadar kudi ta shafin intanet tare da kin biyan hukumomin kasar haraji kamar yadda doka ta tanada
  • Yanzu haka, wasu majiyoyi sun bayyana cewa ana shirin dawo da Nadeem Anjarwalla Najeriya a makon nan domin ci gaba da fuskantar shari'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kenya -Jami’an ‘yan sandan kasar Kenya sun cafke shugaban kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla bayan ya tsere daga gidan yarin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Yanzu haka hukumar yan sanda ta kasa da kasa na shirin dawo da shi Najeriya inda zai ci gaba da fuskantar tuhume tuhume da dama ciki har da hada-hadar kudi ta kafar intanet ba bisa ka’ida ba.

Nadeem Anjarwalla ya tsere daga Najeriya
Yan sandan kasa da kasa na shirin dawo da Nadeem Anjarwalla Najeriya a makon nan Hoto: UGC
Asali: UGC

Wasu jami’an gwamnatin Kenya da su ka nemi a sakaye sunayensu sun tabbatarwa da jaridar Punch cewa yanzu haka Nadeem yana hannun rundunar ‘yan sandan kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Nadeem Anjarwalla zai dawo Najeriya?

A cewar majiyoyin sun bayyana cewa ana shirin dawo da daya daga jiga-jigan kamfanin Binance din Najeriya a makon da mu ke ciki.

Majiyar ta bayyana cewa:

“Rundunar ‘yan sandan Kenya ta kama shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla, kuma INTERPOL za ta mayar da shi Najeriya a makon nan.”

Wata majiyar a gwamnatin kasar Kenya da ta tabbatar da lamarin ta ce :

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Hukumar NIS ta umarci jami'ai su sanya ido kan motsin tsohon gwamna

“Kamar yadda mu ka bayyana a baya, za a mayar da Anjarwalla, an kama shi a Kenya, kuma za a mayar da shi Najeriya a cikin makon anan.”

Anjarwalla na rike da shaidar dan kasa ta Birtaniya da kasar Kenya, kamar yadda Ripples Nigeria ta ruwaito.

Shugaban kamfanin Binance ya tsere

Kun ji a baya cewa Nadeem Anjarwalla, daya daga shugabannin Binance ya gudu daga gidan kurkuku inda ake tsare da shi a Najeriya lokacin da ya je sallah.

Rahotanni sun bayyana cewa ana tuhumar kamfanin na Binance da gudanar da cinikayyar kudi ta shafin intanet a Najeriya ba tare da biyan haraji ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel