Bayan kimanin shekaru 2, za'a daina kayyade adadin masu shiga Masallatan Makkah da Madina

Bayan kimanin shekaru 2, za'a daina kayyade adadin masu shiga Masallatan Makkah da Madina

  • Nan da kwanaki biyu, an janye dokar kayyade masu shiga Ibadah Makkah da Madina
  • Gwamnatin Saudiyya ta sassauta dokar ne bayan samun saukin yaduwar cutar Korona
  • Amma ta sanya wasu sharruda gida uku ga masu niyyar shiga

Makkah - Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa nan da kwana biyu za'a cire dokokin kayyade adadin wadanda ke shiga cikin Masallatan Makkah da Madina don Ibadah.

Wannan na zuwa kimanin shekaru biyu da aka kayyade adadin masu shiga sakamakon bullar cutar Korona.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta sanar da cewa fari daga ranar Lahadi mai zuwa, za'a bude Masallatan biyu wa kowa ya shiga.

A cewar Haramain Sharifain, Ma'aikatar tayi sanarwan ranar Juma'a, 15 ga Oktoba, 2021.

Read also

Da dumi-dumi: Za'a daina bada tazara a sahun Sallah daga gobe Lahadi a Makkah da Madina

Jawabin yace:

"Ma'aikatar harkokin cikin gida a ranar Juma'a ta sanar da bude Masallatan Harama biyu daga ranar Lahadi, 11 ga Rabi Al Awwal 1443 wanda yayi daidai da 17 ga Oktoba, 2021."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sharrudan da aka sanya yanzu sune:
1. Wadanda sukayi rigakafin Korona kadai zasu shiga kuma su kasance masu shekaru akalla 12
2. Wajibi ne sanya takunkumin fuska cikin masallatan Makkah da Madina kowani lokaci
3. Wajibi ne neman izini don Sallah, Umrah, Sallah a Rawdah da ziyara a kan manhajar Tawakalana ko Eatmarna"

Bayan kimanin shekaru 2, za'a daina kayyade adadin masu shiga Masallatan Makkah da Madina
Bayan kimanin shekaru 2, za'a daina kayyade adadin masu shiga Masallatan Makkah da Madina
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel