Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya

Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya

  • Mehmet Ozyurek dan asalin kasar Turkiyya mai shekaru 71 shi ne mahaluki rayayye da ya fi kowa tsayin hanci a duniya
  • A tsayin hancinsa da aka gwada, ya kai inci uku da rabi, wanda ya yi daidai da sentimita takwas da digo takwas
  • A halin yanzu, kundin tarihin Guiness sun ba shi kambun girmamawa na wanda ya fi kowa zankadeden hanci a duniya

Turkiyya - Bincike ya bankado rayayyen dan Adam da ya fi kowanne mutum tsayin hanci a duniya. An gano cewa tsayin hancinsa ya kai inci uku da rabi.

A shekaru goma da suka gabata, wani mutum mai suna Mehmet Ozyurek dan asalin kasar Turkiyya mai shekaru 71 ya kafa tarihi.

Shi ne mutum na farko da ya shiga kundin tarihin duniya na Guinness a matsayin dan Adam da ya fi kowa tsayin hanci, aminiya Daily Trust ta wallafa.

Read also

Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka

Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya
Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Kamar yadda jaridar The Mirror ta wallafa, a yayin da aka gwada tsayin hancinsa a wani shirin gidan talabiji da aka yi da shi a kasar Italiya, an tabbatar da tsayin hancin Mehmet ya kai sentimita takwas da digo takwas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tsawon zankadeden karan hancin Mehmet da aka gwada shi a wani shirin gidan talabijin a Italiya ya kai sentitimita takwas da digo takwas," in ji jaridar.

Tun a wannan lokacin aka bai wa Mehmet kambun yabo na kundin tarihin Guiness, har yanzu kuwa ba a samu wanda ya zarce sa wurin tsawon hanci ba.

Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya
Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Sai dai kuma, tarihin duniya ba zai manta da wani bawan Allah mai suna Thomas Wedders ba dan asalin yankin Yorkshire na kasar Birtaniya. Shi ne mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya.

Tabbas kundin Guiness ya nuna cewa tsayin hancin Wedders, wanda ya yi rayuwarsa a karni na 17, ya kai sentimita 19, wato inci bakwai da rabi kenan.

Read also

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

Hotunan rayayyen mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya
Wedders, mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a tarihin duniya. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, cikin mutane ya caccaki Abdullahi Ganduje, bayan gwamnan jihar Kanon ya nuna kamar bai san da shi a wurin wani taro ba.

Kamar yadda jaridar ThisDay ta wallafa, taron kaddamar da wani littafi ne wanda fitaccen dan jarida Dr. Amanze Obi ya rubuta, kuma Ihedioha da Ganduje duk sun halarta.

Lamarin ya fara ne lokacin da gwamnan jihar Kano, wanda shi ne babban bako na musamman a wurin kaddamar da littafin ya gaida dukkan jiga-jigan da ke teburi na musamman, amma bai ko duba inda Ihedioha ya ke ba.

Source: Legit

Online view pixel