Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka

Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka

  • A wani taro da aka yi a babban birnin tarayya da ke Abuja, rikici ya barke tsakanin manyan 'yan siyasa biyu na kasar nan
  • Rt. Hon Emeka Ihedioha, tsohon kakakin majalisar wakilai ya watsa wa Gwamnan jihar Kano miyagun habaici
  • Ihedioha, tsohon gwamnan jihar Imo, cike da nuna fushinsa ya soka wa Ganduje maganganu kan ya nuna kamar bai san ya na wurin taron ba

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, cikin mutane ya caccaki Abdullahi Ganduje, bayan gwamnan jihar Kanon ya nuna kamar bai san da shi a wurin wani taro ba.

Kamar yadda jaridar ThisDay ta wallafa, taron kaddamar da wani littafi ne wanda fitaccen dan jarida Dr. Amanze Obi ya rubuta, kuma Ihedioha da Ganduje duk sun halarta.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka
Ihedioha ga Ganduje: Sai Ubangiji ya matsi bakin ka wata rana, za ka tona sirrin ka. Hoto daga Emeka Ihedioha
Asali: Facebook

Lamarin ya fara ne lokacin da gwamnan jihar Kano, wanda shi ne babban bako na musamman a wurin kaddamar da littafin ya gaida dukkan jiga-jigan da ke teburi na musamman, amma bai ko duba inda Ihedioha ya ke ba.

"Yayin da Gwamna Ganduje ya yi jawabinsa, ya zabi kada ya san da zaman Emeka Ihedioha. Ban damu ba. Ya tabbatar da abinda na sani ne kawai".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ihedioha ya juya zuwa gwamnan tare da kara cewa:

"Gwamna Ganduje, ina addu'ar Ubangiji ya ba ka karfin guiwar wata rana ka tona asirin kan ka kuma ka yi gyara da kan ka. Gaskiya ce kadai za ta iya fitar da kai."

Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa

A wani labari na daban, Gwamnan Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aike da karin kasafin kudi har N33.8 biliyan gaban majalisar jihar domin ta amince da shi. Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya karanta wannan bukatar a zauren majalisar jihar Kano a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake korar tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji, daga mukaminsa

Kamar yadda bukatar gwamnan ta bayyana, N3.22 biliyan zai biyan ma'aikata yayin da N9.2 za a kashe su kan bukatun yau da kullum, sai kuma N21.5 biliyan ta manyan ayyuka, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, da karin kasafin N33 biliyan, jimillar kasafin kudin shekarar 2021 za ta tsaya a N231.7 biliyan. Ganduje ya yi bayanin cewa, an miko wannan bukatar ne saboda bukatar da ta taso tabbatar da an cimma manufofi da kuma kammala ayyuka masu matukar amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel