Sharif Lawal
4035 articles published since 17 Fab 2023
4035 articles published since 17 Fab 2023
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kan jami'an 'yan sanda da ke aikin sintiri a jihar Abia. Miyagun sun hallaka Sufeton 'yan sanda da wasu mutum uku.
Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta yi babban kamu bayan daruruwan mambobin jam'iyyun adawa na PDP, APGA da LP sun dawo cikinta. Sun sha alwashin ba da gudunmawarsu.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kakaba sabon harajin N425bn kan wasu bankuna guda bakwai saboda ribar da suka samu.
Ministar harkokin mata a karkashin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi zargin majalisa ta taso ta a gaba ne saboda bashin $500m.
Wani jami'in dan sanda ya yi sanadiyyar raba mahaifinsa da duniya a jihar Borno. Jami'in dan sandan ya hallaka mahaifinsa ne bayan ya bude masa wuta.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa daya daga cikin attajiran abokansa ya fara yi masa dariya kan matsalar da yake fuskanta.s
Gwamnatin jihar Benue karkashin jagorancin Gwamna Hyacinth Alia, ta yi kira ga 'yan bindiga da su ajiye makamansu su zo a tattauna a teburin sulhu.
Hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirika, Alhaji Aliko Dangote, ya yi tayin siyar da matatar man fetur dinsa ga kamfanin NNPCL na Najeriya.
Mazauna karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, sun fito kan tituna domin nuna adawarsu da yadda 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka a yankin.
Sharif Lawal
Samu kari