Sani Hamza
4995 articles published since 01 Nuw 2023
4995 articles published since 01 Nuw 2023
Babbar kotun tarayya ta dakatar da PDP daga gudanar da taron kasa da kuma hana INEC sa ido, bayan korafin Sule Lamido cewa an tauye masa hakkinsa na shiga zabe.
Rikici ya barke a Badagry, bayan jami’in hukumar shige da fice ya harbi wata mata, lamarin da ya sa wasu fusatattun matasa suka kona shingen bincike hukumar.
‘Yan gida daya su 2 da aka sace a Imoga, jihar Edo, sun tsero bayan masu garkuwar su sun yi bacci a daji, yayin da aka nemi gwamnati ta kafa ofishin ‘yan sanda.
Ministan labarai, Mohammed Idris ya roki ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu kan sabuwar takaddamar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka bayan kalaman Trump.
EFCC ta ayyana tsohon ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dala miliyan 14.8.
Kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi kusufi kasa, inda masu jari suka tafka asarar Naira tiriliyan 2.84 yayin da darajar kasuwar NGX ta sauka da 2.9%.
Shehu Sani ya gargadi ƴan Najeriya da sauran ƴan Afirka da aka soke musu biza a Amurka da su koma gida kafin a kama su, yayin da gwamnatin Trump ta soke biza 80,000.
Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa da su tare da lalata sansanin Boko Haram/ISWAP a jihar Borno, inda suka kuma kama mutane 29.
Dr. Wole Oluyede ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Ekiti don zaɓen 2026. PDP ta sha alkawarin kayar da APC saboda gazawar gwamnatin Oyebanji.
Sani Hamza
Samu kari