Muhammad Malumfashi
20437 articles published since 15 Yun 2016
20437 articles published since 15 Yun 2016
Masana'antar fina-finan Nollywood da ke Kudancin Najeriya ta yi bsbban rashi da jaruma Nkechi Nweje ta riga mu gidan bayan bayan gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban rikon kwarya a jihar Rivers, Vice Admiral, Ibok-Ete Ibas ya umarci a biya ma’aikatan kananan hukumomi albashin da suke bi ba tare da bata lokaci ba.
Dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Yusuf Shittu Galambi, ya musanta zargin da ake jifan 'yan majalisa da shi na karbar cin hanci kan dokar ta baci a Rivers.
Malamin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya koka kan rikici sarautar Kano, tsakanin Aminu Ado Bayero da Sanusi II. Ya yi magana kan tarbiyya da tattalin Arewa.
Dakarun sojoji sun yi gumurzu da 'yan ta'addan Lakurawa a jihar Kebbi. Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan kungiyar tare da kwato masu yawa.
Jami'an tsaro sun karyata kai hari jami'ar Maiduguri inda suka bayyana cewa harbe-harben da aka ji sun faru ne a Ajilari da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya.
Jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Agbo Major ta bayyana cewa yarjejeniyarta da ƴan Kwankwasiyya ta kare bayan kammala zaben shugaban kasa na 2023.
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi magana kan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da Bola Tinubu ya yi a makon da ya wuce. Sun fadi dalilin yin shiru kan lamarin.
Jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta gargadi gwamnatin Kano da cewa za ta iya jawo wa kanta dokar ta baci da irin furucin da ta yi a kan Hafsa Ganduje.
Muhammad Malumfashi
Samu kari