Muhammad Malumfashi
21463 articles published since 15 Yun 2016
21463 articles published since 15 Yun 2016
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki hutun aiki na kwanaki 10, zai shafe wannan lokaci a tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya in ji fadar gwamnati.
Jagoran 'yan bindiga a jihar Zamfara, ya fusata inda ya bindige wasu daga cikin mayakansa. Ado Aleiro ya yi kisan ne da kansa kan zargin cin amana.
Tsohon Gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, ya bayyana goyon bayansa ga shugaba Bola Tinubu, tare da alwashin nema masa kuri'un Kudu maso Yamma a zaben 2027.
A labarin nan, za a ji gwamnati ta lissafa wasu jihohi da yankunan da ake sa ran za su gamu da iftila'in ambaliya a cikin kwanaki biyar da za a yi mamakon ruwa.
Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta fitar da wata sanarwa game da kyautar da aka ba daliba Nafisa Abdullahi inda ta ce ba gwamnatin tarayya ba ne ta bayar.
An tabbatar da mutuwar akalla mutane 60 bayan wani jirgin ruwa ya juye mutane kusan 100 a teku, galibin wadanda ke cikin jirgin mata ne da kananan yara.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan matsalar rashin tsarom da ake fama da ita. Ya nuna cewa yana da masaniya kan shugabannin 'yan bindiga.
Gwamnatin Amurka ta gargadi 'yan kasarta kan zuwa wuraren da ke kusa da sansanin soji a Najeriya. Ta soke bizar mutane da dama a Najeriya ba gargadi.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana yadda ta ceto wadansu jihohi 27 na kasar nan daga matsalar gaza biyan albashin ma'aikata.
Muhammad Malumfashi
Samu kari