Muhammad Malumfashi
21443 articles published since 15 Yun 2016
21443 articles published since 15 Yun 2016
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ga gayawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa akwai wasu karin gwamnonin adawa da za su dawo APC.
Majalisar shura ta jihar Kano ta sanar da dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa'azi har sai ya kare kansa a gaban majalisar kamar yadda aka kai kokensa gabanta.
Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da rasuwar Sheikh Bashir Bin Ahmed Siddiq, daya daga cikin manyan malaman da ke koyarwa da Alkur'ani a masallacin Annabi SAW.
Jam’iyyar PDP ta rusa shugabanta a jihohin Akwa Ibom da Cross River, ta kuma nada kwamitocin rikon kwarya yayin da rikicin cikin gida suka jawo babban garambawul.
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutane 26 a hatsarin jirgin ruwan da ya rutsa da yan kasuwa ranar Litinin, Gwamna Ahmed Ododo ya yi ta'aziyya.
Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi afuwa ga mutanen da ke zaman gidan gyaran hali. Gwamnan ya zabo su ne bayan yabawa da halayensu.
Yayin da yajin aikin PENGASSAN ya shiga rana ta biyu, gidajen mai sun rufe a fadin Najeriya, an samu dogayen layuka, sannan wutar lantarki ta fadi kasa da 3,500MW.
Gwamna Francis Nwifuru ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa tafiyar da ya yi zuwa kasashen ketare neman magani ya je, ya ce babu abin da ke damunsa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da wata malamar asibiti bayan ta yi rantsuwar kama aiki. 'Yan bindigan sun bukaci a ba su kudin fansa masu tarin yawa.
Muhammad Malumfashi
Samu kari