Muhammad Malumfashi
20353 articles published since 15 Yun 2016
20353 articles published since 15 Yun 2016
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan rikicin Boko Haram. Ya bayyana cewa ya kamata a dauki kwararan matakai don magance matsalar.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai halarci jana'izar shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwada a Filato. Zai gana da shugabannin Kiristocin Arewa a Jos.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi kira ga Isra'ila ta gaggauta daina kai hari Gaza bayan martanin Hamas kan shirin kawo zaman lafiya a Gabas ta tsakiya.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce Boko Haram ta taba zabar marigayi Muhammadu Buhari a matsayin mai shiga tsakani da gwamnatin tarayya.
Kotu ta yanke wa shahararren mawakin hip-hop, Sean “Diddy” Combs, hukuncin zaman gidan yari na fiye da shekaru huɗu kan tuhumar da ta shafi karuwanci a Amurka.
Tsohon kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa Jonathan ya yi wa Buhari karya ne domin ya samu karbuwa wurin yan Najeriya a 2027.
An shiga tashin hankali a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo yayin da wasu matasa suka lakadawa sarki da dansa dukan tsiya, suka nemi yiwa matar sarki tsirara.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana cewa kowane maniyyaci zai samu ragin akalla N200,000 a hajjin 2026.
Bishop Matthew Hassan Kukah ya ce Najeriya ba za ta kawo ƙarshen ta’addanci da karfin bindiga kaɗai ba, yana mai jaddada bukatar amfani da sulhu da adalci.
Muhammad Malumfashi
Samu kari