Ibrahim Yusuf
5427 articles published since 03 Afi 2024
5427 articles published since 03 Afi 2024
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar sun yi jimamin rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata. Dantata ya rasu a Abu Dhabi yana da shekara 94.
Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya taba bayyana cewa yana fatan cikawa da imani idan lokaci ya yi. Ya yi maganar ne shekara biyu kafin rasuwar shi.
Wani rahoto ya nuna cewa an tilasta tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje yin murabus. An saka Ganduje yin murabus ne domin a jawo Kwankwaso APC.
Gwamnonin jam'iyyar APC 23 sun yi taro na musamman a jihar Edo domin tattauna makomar APC a Najeriya. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan murabus din Ganduje
Wani jigo a APC ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso zai iya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje bayan ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC a Abuja.
Rundunar sojin Najeriya ta ware kwanaki uku domin zaman makoki da jimami kan zaratan sojoji 17 da aka kashe a jihar Neja. An ware kwanakin ne don girmama su
Jam'iyyar APC ta tabbatar da murabus din Abdullahi Ganduje daga shugabancin jam'iyyar. APC ta yi wa Ganduje fatan alheri bayan kammala shugabancin jam'iyya.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani shugaban Fulani a jihar Kogi da ake kira da malam Iliyasu. Harbi matar shi da dan shi yayin harin. Suna asibiti suna kwance.
Sanata Barau Jibrin ya sauya sunan kungiyar goyon bayansa daga Barau zalla zuwa Barau/Tinubu yayin da ake maganar ajiye Kashim Shettima a dauke shi.
Ibrahim Yusuf
Samu kari