Ibrahim Yusuf
5421 articles published since 03 Afi 2024
5421 articles published since 03 Afi 2024
Fadar shugaban kasa ta ce alakar shugaba Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso ba sabuwa ba ce, kuma babu laifi idan sun hada hanya a siyasar Najeriya a gaba.
Majalisar wakilai ta fara muhawara kan shirin dawo da zaben shugaban kasa, gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da na jihohi a rana daya a zaben 2027.
Jam'iyyar SDP ta ce ta sallami Nasir El-Rufa'i daga harkokinta har zuwa shekara 30 masu zuwa. SDP ta ce El-Rufa'i bai taba rajista da ita duk da ikirarin da yake yi.
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana cewa Atiku Abubakar ne jagoran siyasar Arewa duk da cewa ya fita daga PDP zuwa ADC. Ya ce PDP za ta dawo da karfinta.
Wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kudu maso Gabas ta tara wa Tinubu miliyan 200 domin sayen fom din takara a zaben 2027 mai zuwa.
Jami'a tsaro sun kama mutane 22 da ake zargi da shiga kungiyar asiri a jihar Ogun. Cikin mutanen da 'yan sanda suka kama akwai sojoji biyu da wasu mata.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr Muhammad Abubakar da aka fi sani da Dr Dalha Konduga ya rasu a jihar Borno. Malamin ya rasu bayan rashin lafiya.
Rundunar sojin Najeriya ta hallaka wani dan bindiga Dan Dari Biyar da ya shahara da kashe mutane da garkuwa da mutane da gallazawa Hausawa a Sokoto.
Gwamnonin da suka yi mulki a 1999 sun bukaci Bola Tinubu ya samar da ayyuka ga matasa wajen kafa kamfanoni maimakon raba tallafin da bai wuce N5,000 ba.
Ibrahim Yusuf
Samu kari