Ibrahim Yusuf
5404 articles published since 03 Afi 2024
5404 articles published since 03 Afi 2024
Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasar Tanzania. An sanar da sakamakon zaben ne a yau Asabar. Za a rantsar da Samia Suluhu Hassan yau Asabar.
Gwamnatin Najeriya ta yimartani ga Donald Trump kan cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a kasar. Ta ce babu kamshin gaskiya a zargin da Trump ya yi.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya umarci majalisar Amurka ta yi bincike kan zargin kisan Kiristoci da ya ce ana yi a Najeriya. Ya ce ba zai zuba ido ba.
Gwamnatin jihar Borno ta fara amfani da kamfanin hada rabobi da da kayan sola da ake yi a jihar zuwa jihohi. A lokacin Muhammadu Buhari aka kaddamar da cibiyar.
Dan takarar shugaban kasa a SDP a zaben 2023. Adewole Adebayo ya ce babu wani alheri da za a samu a mulkin soja a Najeriya. Ya ce dimokuradiyya ta fi.
Hukumar INEC ta yi karin haske kan cigaba da rajistar jam'iyyu da ta fara. Kungiyoyi 6 sun gaza cika sharuda yayin da 8 suka tafi mataki na gaba.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin kin sayen matataun man Najeriya. Ya ce akwai kungiyoyi da masu kudi da ya kamata su saye matatun NNPLC a Najeriya.
Wasu rahotanni sun ce hukumar EFCC da NFIU sun fara bincike kan yadda aka so amfani da wasu kudi a shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
'Yan kasuwar man fetur sun yi gargadi da cewa kudin litar man fetur zai haura N1,000 saboda sabon tsarin haraji na 15% da Bola Tinubu ya kawo a Najeriya.
Ibrahim Yusuf
Samu kari