Ibrahim Yusuf
5367 articles published since 03 Afi 2024
5367 articles published since 03 Afi 2024
Gwamnatin jihar Kebbi ta yi ta'aziyyar rasuwar mata 13 da yaro 1 a cikin tawagar rakiyar amarya a karamar hukumar Yauri a wani haɗarin jirgin ruwa.
Majalisar Shari'a ta kasa a Najeriya ta yi Allah wadai da zargin da Amurka ta yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ta ce babu gaskiya a zargin kisan Kiristoci.
Masana ilimin taurari sun ce zai yi wahala a iya ganin watan Ramadan a yau Talata 29 ga Sha'aban a Najeriya. Simwal Usman Jibril ya ce zaibyi wahala a ga wata
Ana bukatar kowane Musulmi ya yi shiri na musamman yayin fara azumin watan Ramadan na 2026 domin samun damar yin ibada yadda ya kamata da samun lada sosai a azumi.
Dan kwamitin ganin wata a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibril ya yi karin haske kan matakan da ake bi wajen ganin wata idan rana ta fadi.
Matasa a jihar Rivers sun yi zanga zangar adawa da 'yan Arewa da ke zaune a jihar. Sun bukatar 'yan Arewa su bar jihar bayan wani rikici da ya barke.
Gwamnonin jam'iyyar APC sun fara nuna alamar goyon bayan gwamna Hope Uzodimma zama shugaban majalisar dattawa bayan zaben 2027. Ana fatan zai nemi sanata.
Kungiyar Izala karkashin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta tura malamai tafsiri zuwa jihohin Najeriya da wasu yankunan duniya. Wasu malamai za su fara tafsiri.
Gwamnatin shugaba Donald Trump ta rike kadarorin 'yan Najeriya 8 da ya ce suna da alaka da kungiyar Boko Haram da barna ta yanar gizo. Ya sa musu takunkumi.
Ibrahim Yusuf
Samu kari