Aisha Musa
9391 articles published since 09 Agu 2016
9391 articles published since 09 Agu 2016
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba, ya samu goyon bayan jam’iyyar People's Movement (APM), a matsayin dan takararta na shugaban kasa. Shugaban jam’iyyar Yusuf Mamman, ne ya gabatar da wasikar.
Jam’iyyun siyasa karkashin inuwar Coalition of United Political Parties (CUPP) a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba sunyi korafin cewa yan Najeriya na bikin Kirisimetin 2018 cikin bakin ciki da talauci da gwamnati ta jefa su ciki.
Shugaban kungiyar Qadiriyya a Afrika, Sheikh Qaribullah Nasir-Kabara ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai amana da sauraron matsalolin jama’a. Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a bikin Maulidi.
Hajiya Naja'atu Muhammad wacce ta kasance daya daga cikin wadanda suka ta yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari talla a zaben 2015 ta shaida wa majiyarmu cewa ba wani yaki da rashawa da gwamnatin jam'iyyar tasu ke yi.
Gwamnatin Tarayya mayar da martani ga furucin Shugaban Majalisar Dawatta, Dr. Bukola Saraki kan ikirari da ya yi na cewa kasafin 2019 ba shi da wani alfanu a tattare dashi, tace ba za su tsaya sa-in-sa da Saraki ba akan lamarin.
Labari da muke samu ya nuna cewa wani jami’in dan sanda mai sune Rilwani Bala yace ya nemi sauyin wajen aiki daga jihar Sokoto zuwa Kano. A cewarsa ya nemi wannan chanji na wajen aiki ne domin kawai ya dunga ganin Maryam Yahaya.
Sama da malamin Kiristanci 1000 ne suka hadu a Jos don addu’a akan nasarar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar. Wata kungiyar masoyan Atiku ce ta shirya taron addu'an.
Dan majalisar mai wakiltan mazabar azaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi a jihar Jigawa yayi ikirarin cewa abokan aikin nashi sun shirya munakisa akan shugaban kasar makonni kafin gabatar da kasafin kudin saboda bai basu cin hanci ba.
Wata kotu da ke yankin Karu, Abuja a ranar Juma’a, 21 ga watan Disamba ta yankewa wani dan shekara 23 mai aikin walda, Usman Yongo hukuncin watanni 14 a gidan yari kan satar wata waya a masallaci bayan ya amsa laifinsa.
Aisha Musa
Samu kari