Sama da malamai 1000 suka hadu don yiwa Atiku addu’a

Sama da malamai 1000 suka hadu don yiwa Atiku addu’a

- Malaman Kiristanci 1000 ne suka hadu a Jos don addu’a akan nasarar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar

- Wata kungiya mai suna North Central PDP Coalition For Atiku Abubakar 2019, ce ta shirya addu’an na mussaman

Sama da malamin Kiristanci 1000 ne suka hadu a Jos don addu’a akan nasarar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Wata kungiya mai suna North Central PDP Coalition For Atiku Abubakar 2019, ce ta shgirya addu’an na mussaman wanda aka gudanar a Faith Way Chapel International, Millionaires’ Quarters, Jos, jihar Plateau.

Sama da malamai 1000 suka hadu don yiwa Atiku addu’a
Sama da malamai 1000 suka hadu don yiwa Atiku addu’a
Asali: Facebook

Yayinda yake jawabi a wajen taron, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue wanda ya kasance shugaban kamfen din Atiku Abubakar a arewa ta tsakiya da ya samu wakilcin babban hadiminsa, Dr Joseph Atyo yace “A kokarin ganin Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya na gaba a 2019, muna bukatar Allah a aiki saboda komai mai yiwuwa ne da yardarsa.

“Zabar Atiku kokari ne sake gina kasar, saboda tarin kwarewarsa a matsayin mai masana’antu masu zaman kansu kuma shugaba mai tsoron Allah.

KU KARANTA KUMA: Gwaggwafan lada ga dan Kano da yayi fice a jarrabawar 'yansanda ta bana, tukwuici daga Ganduje

“Muna bukatar dukkanin yan Najeriya musamman Kiristoci su tayamu a wannan addu’a ta hanyar sadaukar da lokacinsu a cocinansu daban-daban domin shiryawa Atiku addu’o’i."

Shugaban cocin Faith Way Chapel International, Rev (Dr) Sam T Alaha, wanda ya jagoranci taron addu’an na musamman yace babu shakka duk wani iko na Allah ne kuma duk me neman mulki toh sai ya nemi albarkar Allah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel