Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

- Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta kwace sannan ta lalata sama da tireloli 30 da aka cika da barasa

- Kakakin hukumar ya bayyana cewa an lalata kwalayen barasa a yammacin ranar Litinin bayan an kama su a Kalebawa a hanyar Danbata da ke yankin Dawakin Tofa

- Dokar jihar Kano dai ta haramta amfani da kayan maye a jihar

Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta kwace sannan ta lalata sama da tireloli 30 da aka cika da barasa.

Kakakin hukumar, Malam Adamu Yahaya, ya bayyana hakan a wata sanarwa a Kano a ranar Talata, 25 ga watan Disamba.

Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa
Source: Twitter

Yahaya ya bayyana cewa an lalata kwalayen barasa a yammacin ranar Litinin bayan an kama su a Kalebawa a hanyar Danbata da ke yankin Dawakin Tofa.

“Dokar jihar Kano lamba 4 na 200 ta haramta yin amfani da kayan maye a jihar.

KU KARANTA KUMA: Idan ana son fita daga wahalar da APC su ka jefa jama’a, a zabi Atiku - Saraki

“Don haka akwai wani umurni da kotun majistare ta bamu na aiwatar da shirin,” cewar shi.

Yahaya ya gargadi masu siyar da barasa da kada su wuce gona da iri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel