Buhari shugaba ne mai amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya

Buhari shugaba ne mai amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya

- Shugaban kungiyar Qadiriyya a Afrika, Sheikh Qaribullah Nasir-Kabara ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai amana

- Sheikh Kabara ya bayyana hakan ne a lokacin bikin maulidin da aka gudanar a Kano

- Ya nuna goyon baya ga shugaban kasa a kokarinsa na daidaita amuran Najeriya akan tafarkin ci gaba

Shugaban kungiyar Qadiriyya a Afrika, Sheikh Qaribullah Nasir-Kabara ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai amana da sauraron matsalolin jama’a.

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin bikin maulidin da aka gudanar a Kano.

Nasiru-Kabara yace shugaba Buhari na da son ci gaban kasar a zuciyarsa sannan kuma ya kamata duk masu son ci gaban Najeriya su mara masa baya.

Buhari shugaba ne mai amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya

Buhari shugaba ne mai amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya
Source: Twitter

Ya tuna cewa a lokacin ziyarar da shugabannin suka kaiwa shugaban kasar a fadarsa a kwanakin baya yace anyi gaggawar magance wasu matsaloli da suka gabatarwa gwamnati.

KU ARANTA KUMA: Bana tsoron Buhari, Allah kadai nake tsoro – Gwamna Amosun

Ya nuna goyon baya ga shugaban kasa a kokarinsa na daidaita amuran Najeriya akan tafarkin ci gaba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa shugaban kasar wanda ya samu wakilin babban sakataren kungiyar TETfund, Dr Abdullahi Baffa-Bichi, ya sake tabbatar da jajircewarsa wajen ci gaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel