Kashe-kashe: Buhari ya ziyarci Zamfara kafin ya fara kamfen a Akwa Ibom – Shehu Sani

Kashe-kashe: Buhari ya ziyarci Zamfara kafin ya fara kamfen a Akwa Ibom – Shehu Sani

Sakamakon rikicin kwanan nan day a yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama a jihar Zamfara, Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta sakiya ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kai ziyarar jaje jihar.

Legit.ng ta rahoto da farko cewa wasu yan fashi a ranar Laraba, 19 ga watan Disamba sun kai farmaki garuruwa uku a karsamar hukumar Birnin Magaji na jihar Zamfara, inda suka kashe mutane da dama.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai wadanda ke aiki a gonakinsu lokacin da aka far masu. Majiyoyi da mumunan abun ya faru akan idanunsu sun bayyana cewa yan fashin sun zo da makamai sannan suka fara bude wuta ga manoman da ke girbe dankalin hausa a garin Garin Haladu.

Kashe-kashe: Buhari ya ziyarci Zamfara kafin ya fara kamfen a Akwa Ibom – Shehu Sani
Kashe-kashe: Buhari ya ziyarci Zamfara kafin ya fara kamfen a Akwa Ibom – Shehu Sani
Asali: UGC

Bayan haka sai shugaba Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Abubakar Baba Sadique, umarnin gaggauta zuwa jihohin Sokoto da Zamfara a yau, Talata, da gobe, Laraba, domin yin kiyasin ta'adin da 'yan ta'adda suka yi a sassan jihohin.

KU KARANTA KUMA: Zamfara: Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama umarnin gaggawa

A jawabin da Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce shugaban rundunar sojin saman zai shafe tsawon kwanaki biyu na hutun bikin Kirsimeti a jihohin.

Don haka sai Shehu Sani yace ba wai kawai umurtan shugaban hafsan sojin sama shugaban kasar zai yi kan ya tafi Zamfara ba kamata yayi ace shi da kansa ya je jihar domin yiwa mutanen jihar jaje kafin ya tafi Akwa Ibom don fara kamfen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel