Saad tsohon gwamnan Jigawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Saad tsohon gwamnan Jigawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Ali Saad Birnin Kusu, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Tuni ya yi rijista a mazabar Birnin Kudu na jam’iyyar

- Yace ya koma APC ne don don samun riba ba sai don bayar da gudunmawa wajen inganta rayuwar jama’a

Ali Saad Birnin Kusu, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sannan tuni ya yi rijista a mazabar Birnin Kudu na jam’iyyar.

Da yake jawabi ga magoya bayansa da suka halarci taron, ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa APC saboda ya samu bayani akan kyawawan tsari na jam’iyya mai mulki, shugabanci da kuma jajircewa wajen ganin ci gaban kasar da gwamnati mai nagarta.

Saad tsohon gwamnan Jigawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Saad tsohon gwamnan Jigawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Source: Depositphotos

Yace: “Na yanke shawarar komawa APC domin na tabbatarwa da mutane martaba da mutunci da ke tattare da sabuwar jam’iyya ta, wadanda za su yi adawa da siyasar batanci, kuma marasa son zuciya da kokarin ganin ci gaban kasar."

KU KARANTA KUMA: Mu kuka da kanmu idan har zaman lafiya yayi kaura a Najeriya – Obasanjo

Saad wanda kasance gwamnan farin hula na farko a jihar Jigawa, ya ci gaba da bayyana cewa komawarsa APC ba wai don cin riba bane, sai don bayar da gudunmawa wajen kawo ci gaba a rayuwar mutane, kasar da kuma jam’iyyar musamman don ganin nasararta a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel