Garin masoyi baya nisa: Wani matashin dan sanda ya nemi chanjin aiki saboda Maryam Yahaya

Garin masoyi baya nisa: Wani matashin dan sanda ya nemi chanjin aiki saboda Maryam Yahaya

- Wani jami’in dan sanda mai sune Rilwani Bala yace ya nemi sauyin wajen aiki daga jihar Sokoto zuwa Kano

- Ya nemi wannan chanji na wajen aiki ne domin kawai ya dunga ganin jarumar fim din Hausa Maryam Yahaya

Labari da muke samu ya nuna cewa wani jami’in dan sanda mai sune Rilwani Bala yace ya nemi sauyin wajen aiki daga jihar Sokoto zuwa Kano.

A cewar jami’in ya nemi wannan chanji na wajen aiki ne domin kawai ya dunga ganin sahibar ransa Maryam Yahaya.

Garin masoyi baya nisa: Wani matashin dan sanda ya nemi chanjin aiki saboda Maryam Yahaya
Garin masoyi baya nisa: Wani matashin dan sanda ya nemi chanjin aiki saboda Maryam Yahaya
Asali: UGC

Maryam Yahaya dai wata sabuwar jaruma ce a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wacce a yanzu tauraronta ke kan haskawa, kasancewarta mai karancin shekaru da kuma tarin kyau.

An tattaro inda jami’in tsaron ke cewa "Ina Son Na zama Daya Daga Cikin Cikakkin Masoyin Maryam Yahaya Shi Yasa Na Shirya Tsaf Domin Neman Transfer Zuwa Kano Da Aiki Saboda Na Dinga Ganinta.

KU KARANTA KUMA: Sama da malamai 1000 suka hadu don yiwa Atiku addu’a

"Kuma Ina Yi Mata Fatan Zama Jaruma Mafi Daukaka A Duniyar Fina Finai Hausa. Kuma Da Duk Nayi Sallah addu'ata Kenan".

Shafin kannywoodcelebrities ce dai ta wallafa wannan labara a shafinta na Instagram.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng