Buhari ne dan takararmu – Jam’iyyar siyasa da ke da nasaba da Gwamna Amosun ta amince da shugaban kasa

Buhari ne dan takararmu – Jam’iyyar siyasa da ke da nasaba da Gwamna Amosun ta amince da shugaban kasa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu goyon bayan jam’iyyar People's Movement (APM), a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019

- Dantalle ne ya amince da Buhari ne a madadin jam’iyyar a lokacin da ya ziyarci shi inda ya samu rakiyan Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun

- Kakakin Buhari ya tabbatar da cewa jam’iyyar wacce ke da nasaba da Amosun ta nuna goyon baya ga Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba, ya samu goyon bayan jam’iyyar People's Movement (APM), a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019.

Shugaban jam’iyyar Yusuf Mamman Dantalle, ne ya gabatar da wasikar amincewar ga shugaba Buhari a Abuja.

Dantalle ya amince da Buhari ne a madadin jam’iyyar a lokacin day a ziyarci shugaban kasar a fadar shugaban kasa inda ya samu rakiyan Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun.

Buhari ne dan takararmu – Jam’iyyar siyasa da ke da nasaba da Gwamna Amosun ta amince da shugaban kasa

Buhari ne dan takararmu – Jam’iyyar siyasa da ke da nasaba da Gwamna Amosun ta amince da shugaban kasa
Source: Facebook

A wani jawabi daga Femi Adesina, kakakin Buhari ya tabbatar da cewa jam’iyyar wacce ke da nasaba da Amosun ta nuna goyon baya ga Buhari.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashe a Zamfara

Buhari ne dan takararmu – Jam’iyyar siyasa da ke da nasaba da Gwamna Amosun ta amince da shugaban kasa

Buhari ne dan takararmu – Jam’iyyar siyasa da ke da nasaba da Gwamna Amosun ta amince da shugaban kasa
Source: Facebook

Goyon bayan na zuwa ne kwanaki kadaban bayan dan takarar da Amosun yafi so na gwamna a jihar Ogun, ya bar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da wasu inda suka koma APM.

Amosun da yake martani akan sauya shekar yace masu sauya shekar za su samu goyon bayansa kuma zai yi masu kamfen amma zai marawa Buhari baya a APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel