Yan Najeriya na bikin Kirisimeti cikin yunwa da talauci - CUPP

Yan Najeriya na bikin Kirisimeti cikin yunwa da talauci - CUPP

- Jam’iyyar CUPP ta yi korafin cewa yan Najeriya na bikin Kirisimetin 2018 cikin bakin ciki da talauci

- Kakakin jam’iyyar kasa, a wata sanarwa ya bayyana cewa al’umman kasar da dama na bikin Kirisimeti da yunwa

- A halin da ake ciki, Shugaban kasa Mummadu Buhari ya jadadda burin samar da Najeriya mai inganci anan gaba

Jam’iyyun siyasa karkashin inuwar Coalition of United Political Parties (CUPP) a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba sunyi korafin cewa yan Najeriya na bikin Kirisimetin 2018 cikin bakin ciki da talauci.

Imo Ugochinyere, kakakin jam’iyyar kasa, a wata sanarwa ya bayyana cewa al’umman kasar da dama na bikin Kirisimeti da yunwa, jaridar Punch ta ruwaito.

Yan Najeriya na bikin Kirisimeti cikin yunwa da talauci - CUPP
Yan Najeriya na bikin Kirisimeti cikin yunwa da talauci - CUPP
Asali: Depositphotos

Ugochinyere ya daura laifin akan abunda ya bayyana a matsayin wahalar tattalin arziki da yan Najeriya ke iki a karkashin wannan gwamnatin mai ci, inda ya kara da cewa masu zabe na da dama a hannunsu kamar yadda zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ke a hanya don haka su kasance masu lura da kyau.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati

A halin da ake ciki, Shugaban kasa Mummadu Buhari ya jadadda burin samar da Najeriya mai inganci anan gaba, a sakon Kirisimeti da ya aikewa yan Najeriya.

Sannan yayiwa Kiristocin Najeriya fatan alkhairi da bikin Kirisimeti cikin aminci, sannan ya bukai suyi koyi da koyarwar annabi Isah wajen wanzar da zaman lafiya tare da yafiya sannan ya bukaci suyi amfani da wannan dama wajen yiwa kasa addu’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel