Kasafin kudin 2019 zai sha zaman jira har sai bayan zabe – Yan majalisa

Kasafin kudin 2019 zai sha zaman jira har sai bayan zabe – Yan majalisa

- Yan majalisa sun yi gargadin cewa kasafin kudin 209 na iya kaiwa a watan Afrilu bayan zabe

- Hakan a bisa ga ra’ayin wasu yan majalisa ne, saboda za su mayar da hankalinsu ga kamfen din zaben 2019

Wasu yan majalisa sun bayyana cewa babu yadda za’a yi majalisar dokokin kasar ta kammla aiki akan kasafin kudin kasar kafin zaben shekara mai zuwa, koda dai sun yi akawarin fara aiki a kai da wur-wuri.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin kula na majalisar dattawa, Sanata Abdulfatai Buhari, yace zai yi wuya a gabatar da kasafin kudin kafin zabe.

Kasafin kudin 2019 zai sha zaman jira har sai bayan zabe – Yan majalisa

Kasafin kudin 2019 zai sha zaman jira har sai bayan zabe – Yan majalisa
Source: UGC

Yace: “Idan muka dawo zama a ranar 6 ga watan Janairu, shugaban majalisar dattawa zai aika wa kwamitinmu da kasafin kudin.

“Zuwa wannan lokacin zabe zai fara gabatowa sannan kuma za’a ta tattaunawa akan manufofin takardar wanda ka iya daukar mako biyu. Hakan na nufin zamu kasance da mako biyu kawai a gaba.

“Tabbacin d azan bayar shine cewa za mu kammala tattaunawa akan manufofin tsakanin lokacin dawowarmu da na zabe.”

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta kawo manufofin da su taimakawa marasa karfi - Dankwambo

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan basussukan gida da waje, Sanata Shehu Sani yace: “Zuwa lokain dawowarmu, zai rage wata daya cif-cif zuwa zabe. Kowani kwamiti zai gayyaci shugabanninsa na hukumomi akan kokarinsu na gabatar da hakokin dake kansu.

“Ba za mu samu damar cimma hakan ba saboda da dama daga cikinmu za su na yin kamfen.

“Abunda za mu iya cimma kawai shine tattauna manufofin kasafin kudin.”

Sai dai kuma tsohon shugaban majalisa, Ali Ndume ya nuna tabbcin cewa za a gabatar da kasafin kudi kafin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel