Buhari ya yi bikin kirsimeti na karshe a mulki - PDP

Buhari ya yi bikin kirsimeti na karshe a mulki - PDP

Yayinda yan Najeriya ke bikin Kirsimeti, kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fada ma yan Najeriya cewa wannan biki na Kirsimeti shine na karshe ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar Independent ta ruwaito cewa Kola Oogbondiyan, daraktan labarai na kungiyar ne ya bayyana hakan a wani sakon Kirsimeti.

Ya bayyana cewa manufofin Atiku Abubakar abu ne da ake nufin nunawa al’umman kasar a aikace.

Buhari ya yi bikin kirsimeti na karshe a mulki - PDP

Buhari ya yi bikin kirsimeti na karshe a mulki - PDP
Source: Twitter

Yace don haka yan Najeriya su yi bikin kirsimeti cikin kwanciyar hankali da burin samun makoma mai kyau anan gaba kadan.

KU KARANTA KUMA: Uba ya ba yarsa me shekara 3 guba saboda ta fiye kuka a Kano

Sai dai kuma kakakin kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa a APC, Mista Festus Keyamo ya yi watsi da barazanar PDP na zamar da wannan Kirsimetin karshe ga gwamnatin Buhari.

Ya bayyana jawabin a matsayin wani mafarki na tsakar rana da kuma tsananin son mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel