Abokan aikina sun yi wa shugaba Buhari ihu ne don bai basu cin hani ba – Hon. Kazaure (bidiyo)

Abokan aikina sun yi wa shugaba Buhari ihu ne don bai basu cin hani ba – Hon. Kazaure (bidiyo)

- Gudaji Kazaure ya yi ikirarin cewa abokan aikinsa sun yiwa Shugaban Muhammadu Buhari ihu a lokacin gabatar da kasafin kudi ne saboda ya ki basu cin hanci

- Yace abokan aikin nashi sun shirya munakisa akan shugaban kasar makonni kafin gabatar da kasafin kudin

- Kazaure yace kafin 2015, al’ada ne shugaban kasa ya ba yan majalisa cin hanci kafin gabatar da kasafin kudin amma saboda shugaba Buhari bai kula da matsin lambarsu ba

Honourable Muhammed Gudaji Kazaure ya yi ikirarin cewa abokan aikinsa sun yiwa Shugaban Muhammadu Buhari ihu a lokacin gabatar da kasafin kudi ne saboda ya ki basu cin hanci.

A wani bidiyo da ke shawagi a yanar gizo, dan majalisar mai wakiltan mazabar azaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi a jihar Jigawa yayi ikirarin cewa abokan aikin nashi sun shirya munakisa akan shugaban kasar makonni kafin gabatar da kasafin kudin.

Sai yace shi da wadanda ke goyon bayan shugaban kasar sunyi nasarar bata masu shirin nasu.

Kazaure yace kafin 2015, al’ada ne shugaban kasa ya ba yan majalisa cin hanci kafin gabatar da kasafin kudi amma saboda shugaba Buhari bai kula da matsin lambarsu ba, sai suka yanke shawarar tozarta shi.

KU KARANTA KUMA:

A baya mun ji cewa kungiyar NANS tayi kira ga Majalisar Tarayya su ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda wulakanci da tazortar sa da su kayi a lokacin da ya gabatar da kundin kasafin kudin shekara mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel