Wasan kwaikwayo gwamnatin Buhari ke yi da sunan yaki da rashawa – Naja’atu

Wasan kwaikwayo gwamnatin Buhari ke yi da sunan yaki da rashawa – Naja’atu

- Wata jigo APC mai mulki, Hajiya Naja'atu Muhammed ta yi zargin cewa babu gaskiya cikin yaki da cin hanci da rashawa

- Naja’atuta kasance ta kasance daya daga cikin wadanda suka ta yiwa Buhari kamfen a zaben 2015

- Ta kalubalanci gwamnatin Buhari a kan rashin gudanar da bincike kan lamarin gwamnan jihar Kano

Wata jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Hajiya Naja'atu Muhammed ta bayyana cewa babu gaskiya cikin yaki da cin hanci da rashawa wanda gwamnatin jam’iyyarsu ke yi a yanzu.

Hajiya Naja'atu Muhammad wacce ta kasance daya daga cikin wadanda suka ta yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari talla a zaben 2015 ta shaida wa majiyarmu ta BBC cewa ba wani yaki da rashawa da gwamnatin ke yi.

Wasan kwaikwayo gwamnatin Buhari ke yi da sunan yaki da rashawa – Naja’atu

Wasan kwaikwayo gwamnatin Buhari ke yi da sunan yaki da rashawa – Naja’atu
Source: UGC

"Mutum nawa aka kama, wasan kwaikwayo ne kawai ake yi," cewar ta.

Sai dai kuma a cikin jawabinsa na gabatar da kasafin kudi a zauren majalisa, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu tarin nasarori a yaki da cin hanci da rashawa, kuma nan ba da jimawa ba 'yan kasar za su ci moriyar kudaden da aka kwato.

KU KARANTA KUMA: Gugar zana: Bayan Allah da Buhari wani kato baya bamu tsoro - Gwamnan APC

Amma Hajiya Naja'atu 'yar siyasa daga jihar Kano ta yi tsokaci game da wasu jerin bidiyon da aka wallafa da ke zargin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudaden da aka ce cin hanci ne daga hannun 'yan kwangila.

Ta kalubalanci gwamnatin Buhari a kan rashin gudanar da bincike kan lamarin, duk da ikirarin da ta ke yi cewa tana yaki da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel