Kotu ta yankewa wani mutum watanni 14 a gidan yari kan satar waya a masallaci

Kotu ta yankewa wani mutum watanni 14 a gidan yari kan satar waya a masallaci

- Wata kotu da ke Abuja ta yankewa wani dan shekara 23 mai aikin walda, Usman Yongo hukuncin watanni 14 a gidan yari

- An dai kama matashin ne da laifin satar wata waya a masallaci

- Mohammed ya ba mai laifin zabin biyan N40,000 a matsayin tara

Wata kotu da ke yankin Karu, Abuja a ranar Juma’a, 21 ga watan Disamba ta yankewa wani dan shekara 23 mai aikin walda, Usman Yongo hukuncin watanni 14 a gidan yari kan satar wata waya a masallaci.

Mai shari’a Sani Mohammed ya yankewa Yongo hukuncin daurin bayan an same shi da laifin sata.

Mohammed ya ba mai laifin zabin biyan N40,000 a matsayin tara.

Kotu ta yankewa wani mutum watanni 14 a gidan yari kan satar waya a masallaci

Kotu ta yankewa wani mutum watanni 14 a gidan yari kan satar waya a masallaci
Source: Depositphotos

Da farko, dan sanda mai kara, Vincent Osuji, ya fada ma kotu cewa wani Shefianu Ibrahim na masallacin Ammar BN Yasir, Karu, Abuja ne ya kai karar lamarin ofishin yan sanda da ke Karu, a ranar 4 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 5 a Zamfara

Osuji ya bayyana cewa mai laifin ya saci shiga masallacin sannan ya sace wata wayar ZTE da aka sa chaji mallakar me karan.

A cewarsa lokacin binciken yan sanda, wanda ake karan ya amsa laifinsa sannan an karbo wayar a hannunsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel