Kasafin kudin 2019: Gwamnatin tarayya ta maida martani akan furucin Saraki

Kasafin kudin 2019: Gwamnatin tarayya ta maida martani akan furucin Saraki

- Gwamnatin Tarayya mayar da martani ga furucin Shugaban Majalisar Dawatta, Dr. Bukola Saraki kan ikirari da ya yi na cewa kasafin 2019 ba shi da wani alfanu a tattare dashi.

- Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta bata bakinta ba wajen yin cecekuce da Saraki ba

- Ya kara da cewa bangaren zartarwa ya sauke nauyin da ke kan sa na kasafin kudi, tunda har ya tsara, kuma an gabatar wa majalisa

Gwamnatin Tarayya mayar da martani ga furucin Shugaban Majalisar Dawatta, Dr. Bukola Saraki kan ikirari da ya yi na cewa kasafin 2019 ba shi da wani alfanu a tattare dashi.

Ministan Labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana a ranar Juma’a, 21 ga watan Disamba cewa gwamnatin tarayya ba za ta bata bakinta ba wajen yin cecekuce da Saraki ba.

Kasafin kudin 2019: Gwamnatin tarayya ta maida martani akan furucin Saraki

Kasafin kudin 2019: Gwamnatin tarayya ta maida martani akan furucin Saraki
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa bangaren zartarwa ya sauke nauyin da ke kan sa na kasafin kudi, tunda har ya tsara, kuma an gabatar wa majalisa.

An ruwaito Saraki na cewa kasafin ba shi da wani tasiri idan aka yi la’akari da kudaden shigar da ake samu da kuma sauran mishkilolin da ke tattare da tafiyar da gwamnati da kuma abubuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA KUMA: Gugar zana: Bayan Allah da Buhari wani kato baya bamu tsoro - Gwamnan APC

Haka jaridar Vanguard ta ruwaito Saraki ya fada a matsayin sa na dan adawa, dan jam’iyyar PDP kuma Daraktan Kamfen na Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar.

Lai ya ce ba za su tsaya sa-in-sa da majalisa ko Saraki ba, tunda su dai a na su bangaren sun yi iyakar yin su, kuma sun yi bakin kokarin su na gabatar da kasafin kudi daidai karfin tattalin arzikin Najeriya.

Lai ya ce gwamnatin Buhari ta cika dukkan alkawurran da ta dauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel