Wata yar'uwa Musulma ta kawata gidan fasto don bikin Kirisimeti a Kaduna
Kamar yadda muka sani addini na daya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa rabuwar kai a kasar. An samu yawan kashe-kashe a fadin kasar wanda mafi akasarinsu na da nasaba da rikicin addini. Don haka wannan mata Musulma na kokarin chanja lamarin daya bayan daya.
Matar mai suna Ramatu Tijani, jakadiyar zaman lafiya ta samu babbar amar yabo kan karamcin da tayi wa wani fasto mai suna Yohanna Buru. Ramatu ta kawata gidan Buru, shugaban cocin Christ Evangelical Church Sabon Tasha, da bishiyoyin Kirisimeti.
Da take hira da manema labarai a ranar Laraba a Kaduna, Ramatu ta bayyana cewa kawata gidan faston da tayi da kayan alatu don karfafa zaman lafiya da fahimta ne a tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya.
A cewar Ramatu wacce ta shahara a bangaren sasanta rikici a Afrika, daga Musulmi har Kirista yayan Adam da Hawaú ne kuma duk Allah daya suke bautamawa kuma suna da litattafai da suke bi.
KU KARANTA KUMA: Buhari zai fara kamfen din 2019 a Akwa Ibom
Ta shawarci mutane da su wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Yayinda yake yabama karamci irin na Ramatu, faston yace ita ce mutun na farko da aka ta fara bayar da gudunmawa ga coci, yara da matada mazajensu suka mutu.
Yayi addu’a kan Allah ya yi mata albarka sannan ya saka mata da alkhairi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng