Aisha Musa
9391 articles published since 09 Agu 2016
9391 articles published since 09 Agu 2016
Jaridar New York Times tayi ikirarin cewa tana da wani bidiyo da ke nuna jami’an rundunar sojoji a yayinda suke harbin mambobin kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a wanda basu jiba basu gani ba sannan ba wai suna da makamai bane.
Babban sakataren labarai na jam’iyyar Peoples Democratic Party na kasa, Mista Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa kamata yayi shugaba Buhari ya koma gidansa na Daura, jihar Katsina, inda yace shugaban kasar zai fi samun hutu.
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba ya amince da sunayen mutum 12 a hkumar masajlisar sokokin kasar (NASC). Majalisar dattawan ta bayyana cewa za’a gabatar da shugaban ga Shugaba Buhari.
Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kai hari inda suka kashe mutane 14 sannan sun raunata wasu 17 a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba a kauyen Unguwan Paa-Gwandara da ke karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna.
Balaraba Ibrahim Stegert, wata tsohuwar hadimar Rabiu Musa Kwankwaso ta bar jam’iyyar PDP a ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba. Yayinda ake gwagwarmayar siyasa a jihar Kano, Balaraba, babbar hadimar Kwankwaso ta koma jam'iyyar APC.
Atiku Abubakar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za su cika alkawarin da suka daukarma kudu maso gabas na samar da shugaban kasa a 2023 idan suka marawa Buhari baya a shekarar 2019
Shahararriar jarumar na ta masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayar soyayyarta da jarumi Adam A. Zango, a cewarta a baya sun yi soyayya da shi, sai dai yanzu mutunci kawai suke yi.
Shugaban Jami’ar Crawford, kuma tsohon Shugaban Jami’ar Lagas, Farfesa Oye Ibidapo-Obe, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na kashe kimanin naira tiriliyan daya a duk shekara wajen tafiya kasashen waje domin yin karatun digiri.
Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 23 akan auren zaurawa 3,000 da za’a gudanar a jihar. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga kwamishinan bayanai na jihar, Malam Mohammed Garba a Kano a ranar Laraba, 12 ga watan Disamba.
Aisha Musa
Samu kari