Aisha Musa
9391 articles published since 09 Agu 2016
9391 articles published since 09 Agu 2016
Gamayyar jam’iyyun hadin gwiwa ta Coalition of United Political Parties (CUPP) ta bukaci ayi wa dukkanin yan takarar shugaban kasa a zaben 2019 ciki harda shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar gwajin hankali.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ba babban jigon jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, da kuma babban attajirin dan kasuwan nan kuma biloniya Aliko Dangote mukamai a kungiyar kamfe din dan takararta na shugaban kasa a 2019.
Kungiyar makiyayan Miyetti Allah ta bayar da tabbacin kawo wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’u miliyan 20 a zaben 2019. Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammadu Kirowa, yayi wannan alkawarin a wajen taron kungiyar.
Akalla mambobin jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP) 50,000, ciki harda wani tsohon hadimin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Party (APC), a jihar Sokoto.
Hukumar tashohin jiragen ruwa na Najeriya tace tana tsimayin jiragen ruwa 31 da zai kawo kayayyakin man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani a tashar jirgin ruwa na Apapa da kuma Tin Can Island a tsakanin Disamba da Janairu.
sohon gwamnan jihar Lagas a mulkin soja, Buba Marwa ya bayyana cewa duk masu kokarin ganin sun mamaye fadar shugaban kasa ta Villa su jira har 2023 domin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo mulki a shekarar 2019.
Kungiyar Kiristocin Najeriya ta gargadi Gwamna Nasir El-Rufai akan hukunta babban faston cocin Dunamis International Gospel Centre, Dr Paul Enenche. CAN ta ce gargadin ya zama dole saboda rahotannin cewa za a gurfanar da Enenche.
Shugaban kungiyar kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari na Next Level, Honourable Umar Waziri Kumo, ya bayyana cewa mutanen yankin arewa maso gabas za su marawa Buhari baya kwansu da kwarkwatansu don ganin yayi nasara a 2019.
Fadar shugaban kasar Najeriya ta saki wani gagarumin gargadi ga masu rike da mukaman siyasa, da jami’an gwamnati da jam’iyya kan su daina aragizo don samun rara ta hanyar rashawa da kuma amfani da sunan Buhari wajen neman kudi.
Aisha Musa
Samu kari