Ka mika kanka ga yan sanda – Shehu Sani ya bukaci Dino Melaye

Ka mika kanka ga yan sanda – Shehu Sani ya bukaci Dino Melaye

- Sanata Shehu Sani ya shawarci abokin aikinsa, Sanata Dino Melaye da ya mika kanshi ga hukumar yan sanda

- Ana dai ta tsere a tsakanin rundunar yan sandan Najeriya da dan siyasan jihar Kogin

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya shawarci abokin aikinsa, Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta yamma a majalisar dokokin tarayya da ya mika kanshi ga hukumar yan sanda.

Shehu Sani ya bayar da shawarar ne biyo bayan tseren da ake yi tsakanin rundunar yan sandan Najeriya da dan siyasan jihar Kogin.

Ka mika kanka ga yan sanda – Shehu Sani ya bukaci Dino Melaye

Ka mika kanka ga yan sanda – Shehu Sani ya bukaci Dino Melaye
Source: Depositphotos

Jami’an rundunar yan sandan Najeriya na a gidan Dino Melaye a yanzu haka domin kama shi akan zargin harbin wani jami’in dan sanda, Sajent Danjuma Saliu, wanda ke aiki da yan sandan tafi da gidanka na 37 a lokacinda yake bakin aiki a Aiyetoro Gbede, hanyar Mopa da ke Kogi.

Sani wanda ya bukaci Melae da ya gabatar da kanshi ga yan sanda ya wallafa a shafin twitter cewa: “Yan sanda su kawo karshen mamayar da suka kai gidan Dino sannan Sanatan ya gabatar da kansa gay an sanda da tawagar doka. Takun sakan na bata suna yan sanda, gwamnati da ma kasa baki daya.”

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga

A baya mun ji cewa Dino ya yi alkawarin mika kansa ga 'yan sanda cikin mako mai zuwa. A cewar Channels TV, A ranar Juma'a 28 ga watan Disamba, dan majalisar ya ce babu laifin da ya aikata saboda haka babu wani dalilin da zai sa ya rika kauracewa 'yan sanda.

Ya ce babu bukatar 'yan sandan su mamaye gidansa domin zai mika kansa ga jami'an 'yan sanda da zarar ya dawo garin Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel