Mafarauta sun fatattaki Boko Haram daga wani gari a Yobe

Mafarauta sun fatattaki Boko Haram daga wani gari a Yobe

- Mayakan Boko Haram sun kai mamaya Buni-Gari, wani gari a jhar Yobe

- Sai dai wasu mafarauta sun sha karfinsu inda mayakan suka ja da baya suka tsere

- An tattaro cewa yan ta’addan sun kai farmaki ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Lahadi

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne da suka kai mamaya Buni-Gari, wani gari a jhar Yobe, sun haduda daidai da su lokacin da wasu mafarauta suka yi arangama das u a wani musayar wuta da suka yi a ranar Lahadi.

Wani mazaunin garin wanda ya bayyana hakan ga jaridar TheCale yace yan ta’addan sun kai farmaki ne da misalin karfe 5 na yamma.

Mafarauta sun fatattaki Boko Haram daga wani gari a Yobe
Mafarauta sun fatattaki Boko Haram daga wani gari a Yobe
Asali: Twitter

Ya baana cewa koda dai babu sojoi a kasa lokcin da suka kaddamar da harin, mafarauta sun yi nasarar fatattakar yan ta’adda bayan sun far masu da karfi.

Wani majiya ya ce koda dai an kora yan ta’addan daga garin, Buni-Gari ya zama wayam.

“Mutane da dama sun gudu zuwa Buni-Yadi akan tsoron cewa yan ta’addan na iya sake dawowa don kaddamar da mumunan hari,” inji shi.

“Buni-Yadi ya fi Buni-Gari tsaro. Akwai sojoji a chan.”

KU KARANTA KUMA: Marigayi Shehu Shagari bai taba kiran kowa barawo ba - Shehu Sani

A wani lamari na daban, mun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwa shida a jihar Borno.

Daraktan labarai na rundunar, Birgediya Janar Sani Usman, ya karyata rahoton a wani sako da ya aikewa Channels TV a ranar Litinin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel