CUPP ta bukaci ayi ma Buhari, Atiku gwajin lafiyar kwakwalwa gabannin zaben 2019

CUPP ta bukaci ayi ma Buhari, Atiku gwajin lafiyar kwakwalwa gabannin zaben 2019

- Jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta bukaci ayi wa dukkanin yan takarar shugaban kasa a zaben 2019 gwajin lafiyar kwakwalwa

- Kakakin kungiyar Imo Ugochinyere, ta bayyana cewa duk wanda ya gaza cin wannan gwajin toh lallai kada ma a bari yayi takara a zaben 2019

- Ugochinyere ya bukaci bukaci shugaba Buhari da ya yawaita yin jawabi ga ýan Najeriya da kuma ýan jarida musamman ta shafin hiran shugaban kasa da kafofin watsa labarai

Gamayyar jam’iyyun hadin gwiwa ta Coalition of United Political Parties (CUPP) ta bukaci ayi wa dukkanin yan takarar shugaban kasa a zaben 2019 ciki harda shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar gwajin lafiyar kwakwalwa.

Kungiyar da ta sanar hakan a wani jawabi da ta saki a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba ta hannun kakakinta, Imo Ugochinyere, ta bayyana cewa akwai bukatar yin gwajin domin tabbatar da lafiyar kwakwalwar yan takarar shugaban kasa kafin zabe.

CUPP ta bukaci ayi ma Buhari, Atiku gwajin hankali gabannin zaben 2019

CUPP ta bukaci ayi ma Buhari, Atiku gwajin hankali gabannin zaben 2019
Source: Depositphotos

Kungiyar ta bayyana cewa duk wanda ya gaza cin wannan gwajin toh lallai kada ma a bari yayi takara a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Kan mu daya da Atiku wajen ganin mun yi waje da APC – ‘Dan takaran Gwamnan Filato

“Wannan gwajin na da matukar muhimmanci sannan dukkanin yan Najeriya masu fatan ci gaban kasar su bi sahun wannan kira domin bayyana gaskiyar abunda ke lullube a halin da yan Najeriya ke ciki,” inji CUPP.

Kakakin jam’iyyar ya kuma bukaci shugaba Buhari da ya yawaita yin jawabi ga ýan Najeriya da kuma ýan jarida musamman ta shafin hiran shugaban kasa da kafofin watsa labarai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel